Barcelona ta farfaɗo ta doke ƙungiyar Carzola, Oviedo
Barcelona ta farfado daga baya ta kauce wa shan kunya a hannun daya daga cikin na karshen tebur a Laliga Real Oviedo, inda ta rama kwallo daya da mai masaukinta ta sa mata a raga har kuma ta kara biyu aka tashi 3-1.
Miniti 33 da wasa Alberto Reina ya ribaci kuskuren mai tsaron ragar Barcelona Joan Garcia, ya daga ragar bakin ya sa Oviedo gaba, to amma bayan hutun rabin lokaci Barcelona ta ce ruwa ba sa'an kwando ba ne, inda 'yna wasanta Eric Garcia, da Robert Lewandowski da Ronald Araujo suka fitar da ita kunya da kwallo uku.
Wannan nasara ta sa Barcelona ci gaba da wasa ba tare da an doke ta ba a wannan kakar ta bana.
Tsohon danwasan kuma na tsakiya na Sifaniya Santi Cazorla mai shekara 40, ya shiga wasa tun da farkon take leda a karon farko a gasar ta La Liga ta bana a kungiyar.
A 2003, ya bar Real Oviedo din kungiyar da ya fara yana yaro a dole saboda saboda matsalar kudi.
Ya koma kungiyar a 2023, kuma a bara ya taimaka mata ta sake komawa babbar gasar ta Sifaniya a karon farko tun 2001.
Barcelona ta ci gaba da zama ta biyu a tebur da maki 16 a wasa shida, inda maki biyu yake tsakaninta da Real Madrid ta daya.
Ita kuwa Real Oviedo ta kasance ta 18 a teburin mai kungiyoyi 20, inda take da maki 3, Mallorca da Girona da take samansu suna da maki biyu kowacce.