Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 06/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 06/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello da Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Nan za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Kuna iya duba ƙasa domin karanta rahotonnin da muka kawo a yau daga sassan duniya - kafin mu zo da wasu gobe da safe a wani shafin daban.

  2. 'Yansandan Saudiyya sun kama ƴan ƙasar waje da zargin karuwanci a Madina

    'Yansandan Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    An kama wasu mutane ƴan asalin ƙasar waje uku, cikinsu har da mata biyu, bisa zargin "karuwanci" a wani gida da ke birnin Madina na ƙasar Saudiyya.

    Jami'an ƴansandan birnin Madina ne suka kama mutanen lokacin wani samame da suka kai tare da hadin gwiwar sashen kula da tsaron al'umma da yaƙi da safarar mutane.

    Ƴansanda sun ce an miƙa mutanen da ake zargi ga masu gabatar da ƙara bayan bin hanyoyin shari'a da suka dace.

    Madina ne gari na biyu mafi tsarki a Saduiyya da ma duniyar Musulmi bayan Makkah, kuma aikata laifi irin wannan a garin ba ƙaramin saɓo ba ne a mahangar Musulunci.

  3. Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 176 a jihohin Najeriya 21

    Wani ɓera a ɗakin gwaji

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum 176 sakamakon cutar zazzaɓin Lassa a faɗin jihohin ƙasar 21 cikin wata 10.

    NCDC ta ce adadin mutanen da cutar ke kashewa ya ƙaru daga kashi 16.6 cikin 100 a 2024 zuwa 18.4 a 2025 duk da raguwar masu kamuwa da cutar a tsakanin.

    Hukumar ta ɗora alhakin mutuwar kan rashin kai rahoto da wuri, da rashin neman taimakaon likitoci.

    Kazalika, ƙarin mutum 955 ne daga cikin 8,367 da aka gwada suka kamu da cutar ta Lassa a 2025, inda jihohin Ondo, Bauchi, Edo, Taraba suka zama cibiyar cutar da kashi 88 cikin 100 na duka mutanen.

  4. Za mu dawo da doka da oda a Kamaru - Paul Biya

    Paul Biya

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Kamaru Paul Biya ya yi alƙawarin dawo da doka a ƙasar bayan tashin hankalin da aka samu bayan zabe.

    Mista Biya mai shekara 92 wanda ya kama aiki a karo na takwas, ya ɗaura alhakin tashin tashinar kan abin da ya kira yansiyasa "marasa hankali".

    Bayyana Mista Biya a matsayin wanda ya yi nasara a zaben ta tunzura gudanar da zanga-zanga mai muni da nuna tirjiya, wadda ta kai ga mutuwar masu zanga-zangar.

    Sai dai a jawabinsa na kama aiki, shugaban ya jinjina wa jami'an tsaron kasar.

    Bayan shekara 43 yana mulki, shugaban ya sake nanata aniyarsa ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi mata da matasa, tare da alkawarin kawo ƙarshen cin hanci.

  5. Ina tabbatar muku za mu kawo ƙarshen ta'addanci - Tinubu

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da sauran ƙasashen duniya "ta hanyar difilomasiyya" game da matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta a yanzu.

    Kalaman shugaban na zuwa ne a lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ke barazanar kutsawa Najeriyar domin kai wa 'yanbindiga hare-hare bayan ya zargin gwamnatin Tinubu da ƙyale su suna "yi wa Kiristoci kisan gilla"

    Da yake magana yayin zaman majalisar ministocinsa a yau Alhamis, Tinubu ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta kawo "ta'addanci".

    "Duk da ƙalubalen irin na siyasa da fargabar da mutanenmu ke ciki, muna ci gaba da tattaunawa da ƙawayenmu, muna tattaunawa a difilomasiyyance," in ji shi.

    "Ina tabbatar muku cewa za mu kawo ƙarshen ta'addanci. Abin da muka saka a gaba shi ne cigaba da ayyuka ido buɗe bisa manufarmu ta Sabunta Fata [Renewed Hope] domin gina Najeriya mai yalwa."

    Wannan karon farko da aka ga sugaban yana magana kan yaƙi da ta'addanci a fili tun bayan zargin da Trump ya yi kan Najeriya.

  6. Guguwar Kalmaegi ta isa Vietnam bayan mummunar ɓarna a Philippines

    Guguwar Kalmaegi

    Asalin hoton, EPA

    Guguwar Kalmaegi mai ɗauke ruwan sama da iska mai ƙarfi ta isa tsakiyar Vietnam bayan ya yi gagarumin ɓarna a Philippines.

    Ma'aikatar kula da muhalli ta kasar ta ce ana samun iska mai karfi da ke gudun kilomita 149 duk sa'a a sassan kasar.

    Ana hasashen sa'o'i masu zuwa za su zama masu hadarin gaske. Tuni aka kwashe mutane da dama daga yankunan da ke kusa da gabar ruwa.

    Mamakon ruwan mai haɗe da iska mai karfi ya halaka aƙalla mutum 114 a Philippines, inda tuni aka ayyana dokar ta-baci a can.

    Wani mazaunin Philippines ya ce "taɓon da ya taru ya kai inci 12, kuma ruwan ya yi yawan da ya kai har rufin gidajenmu".

  7. Tinubu ya rantsar da sababbin ministoci

    Shugaba Tinubu da Kingsley Tochukwu Udeh

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Shugaba Tinubu da Kingsley Tochukwu Udeh

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da Bernard Mohammed Doro da Kingsley Tochukwu Udeh a matsayin ministoci.

    Tun mako biyu da suka wuce ne majalisar tarayya ta amince da Mista Doro domin maye gurbin Farfesa Nentawe Yilwatda daga jihar Filato, wanda ya zama shugaban jam'iyyar APC na ƙasa mai mulkin Najeriyar.

    Sai a yau Alhamis ne kuma majalisar ta amince da naɗin Kingsley Tochukwu Udeh wanda zai maye gurbin Uche Nnaji daga jihar Enugu, wanda ya sauka daga muƙamin ministan kimiyya bayan zarge-zargen gabatar da shaidar karatu ta bogi.

    Tinubu ya rantsar da ministocin ne jim kaɗan kafin fara taron majalisar zartarwa a fadar shugaban da ke Abuja.

    Shugaba Tinubu da Bernard Mohammed Doro

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Shugaba Tinubu da Bernard Mohammed Doro
  8. Gwamnan Katsina Dikko Radda ya gabatar da kasafin kuɗi na naira biliyan 897.9

    Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda

    Asalin hoton, @dikko_radda/X

    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda ya gabatar da ƙudirin kasafin kudin shekarar 2026 mai kimanin Naira biliyan 897.9 ga majalisar dokokin jihar.

    Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa kasafin kudin na bana shi ne mafi shiryawa tare da shigar da ra’ayoyin jama’a fiye da kowane lokaci a tarihin jihar.

    A cewar gwamnan, an kasafin laƙabi da taken “Gina Makomarku III” domin ya nuna yadda aka gina shi ne kan bukatun al’umma da suka fito kai tsaye daga ƙananan hukumomi da mazaɓu

    Ya ce sama da mutum 71,000 daga mazabu 316 ne suka bayar da gudummawa ta hanyar bada shawara da bukatun da suka ke so gwamnatin ta mayar da hankali a kai.

    Gwamnan ya bayyana manyan bangarorin da aka fi ware kudi da suka haɗa da "ilimi naira biliyan 156.3, aiki da gidaje naira biliyan 117.1, noma naira biliyan 78.6, lafiya naira biliyan 67.5, albarkatun ruwa naira biliyan 62.8 da muhalli naira 53.8.

    ...

    Asalin hoton, @dikko_radda/X

    Hakan ya sanya ilimi ya zama fannin da aka fi warewa kudi, yayin da gwamnati ke ƙara zuba jari domin inganta makarantu da ingancin koyarwa.

    Ya ce fiye da kashi 80 cikin 100 na kasafin kudin an ware shi ga aiyukan raya kasa musamman a fannonin gine-gine da ilimi da lafiya da ci gaban al’umma.

    Gwamnan ya ce "hakan zai taimaka wajen samar da dama ga matasa da raya yankuna daban-daban da kuma ƙarfafa rayuwar jama’a a dukkan kananan hukumomin jihar."

  9. Binciken BBC kan iƙrarin 'kisan Kiristoci' a Najeriya da Trump ya yi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ta kai wa Najeriya hari domin dakatar da abun da ya kira kashe Kristoci a Najeriya ba hakanan ta faru ba.

    Watanni da dama kenan da masu fafutuka da ƴan siyasa a Washington ke zargin cewa masu iƙirarin jihadi suna harin Kiristoci a Najeriya.

    Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da wasu hujjojin da aka dogara da su na iƙirarin ba.

    Amma BBC ta gano cewa wasu alkaluman da ake amfani da su wajen tabbatar da wannan zargi suna da wahalar tabbatarwa da rashin tabbas.

    A watan Satumba, shahararren mai gabatar da shiri Bill Maher ya kira abin da ke faruwa da "kisan ƙare dangi". Ya ce Boko Haram sun kashe fiye da mutane 100,000 tun 2009, sun kuma kona majami'u 18,000.

    Alkaluma irin waɗannan sun yaɗu sosai a shafukan sada zumunta.

    Sai dai gwamnatin Najeriya ta yi watsi da iƙirarin tana mai bayyana shi da jirkita gaskiyar abun da ke faruwa.

  10. An rantsar da Paul Biya a matsayin shugaban Kamaru karo na takwas

    ...

    An rantsar da Paul Biya mai shekaru 93 a matsayin shugaban ƙasar Kamaru karo na takwas a majalisar dokokin ƙasar da ke Yaoundé.

    Ya shafe shekaru 43 yana mulki, kuma yanzu zai fara wani wa'adi na tsawon shekara bakwai.

    Biya wanda shine shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na ƙuri’un zaɓe, yayin da abokin hammayarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar ƙasa.

    Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaɓen yana zargin cewa an yi maguɗi,wanda hukumomi suka musanta.

    Lamarin dai ya janyo zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar inda aka yi asarar rayuka da dukiyoyi.

    ...
    ...
    ...
  11. Shugabar Mexico za ta kai ƙarar mutumin da ya taɓa mata ƙirji a bainar jama'a

    ...

    Asalin hoton, Juan Abundis/ObturadorMX/Getty Images

    Shugabar ƙasar Mexico, Claudia Sheinbaum, ta ce za ta maka wani mutum kotu bayan ya taɓa mata ƙirji tare da yunƙurin sumbatarta a cikin dandazon jama'a lokacin da take jawabi ga magoya bayanta.

    A bidiyon da aka ɗauka da wayar hannu a ranar Talata, an ga mutumin ya kusanto ta daga baya inda yayi ƙoƙarin sumbatarta a wuya tare da dafa jikinta.

    Nan take ta yi saurin matsawa gefe, sannan wani daga tawagarta ya shiga tsakani.

    Hukumar tsaro ta tabbatar da cewa an kama mutumin.

    A wata hira da ‘yan jarida ranar Laraba, Sheinbaum ta ce idan har za a iya yin haka ga shugabar ƙasa a bainar jama’a, to menene zai faru da sauran mata a ƙasar?

    Ta ce ta ɗauki wannan matakin kotu ne saboda irin wannan cin zarafin abu ne da mata da dama ke fuskanta a Mexico, kuma ita kanta ta taɓa fuskantarsa tun kafin ta zama shugaba.

    Ta kuma bayyana cewa akwai rahoton cewa mutumin da aka kama ya yi wa wasu mata a cikin taron irin wannan cin zarafin, shi ya sa ta ga ya dace a ɗauki mataki.

    Ta ce dole a kafa iyaka domin kare mata daga irin wannan dabi’a.

  12. Yara biyu sun mutu cikin rijiya a Kano

    ...

    Wasu yara biyu sun rasa rayukansu bayan sun faɗa cikin rijiyoyi a jihar Kano.

    Ɗaya daga cikin yaran wani yaro ne mai suna Ahmad Abdurashid wanda ke da shekara 6 ya fadɗa ne a rijiya a unguwar Dandishe Tsamiyar Goodluck, karamar hukumar Dala, yayin da ɗayar kuma mace ce mai kimanin shekaru takwas da ta faɗa a rijiya ita ma a ƙauyen Kashirmo, kusa da Sarkakiya a karamar hukumar Dawakin Tofa.

    Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin yaron Ahmad ya faru ne a safiyar Laraba.

    "Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:02 na safe cewa yaro ya faɗa cikin rijiya, inda nan da nan hukumar ta tura tawagar ceto zuwa wurin."

    "Ko da aka ciro yaron daga cikin rijiyar, ya riga ya rasu, sai muka miƙa gawar shi ga mahaifinsa Abdulrashid." in ji kakakin.

    Abdullahi ya ce ana gudanar da bincike kan musabbabin afkuwar lamarin inda ya kuma shawarci mazauna yankin da su rufe rijiyoyinsu yadda ya kamata tare da guje wa tona rijiyoyi a bakin hanya domin kauce wa irin waɗannan haɗurran, musamman a kauyuka.

    Game da yarinyar da ta faɗa rijiaya a Kashirmo, hukumar ta ce an samu kiran gaggawa ranar Talata da safe, amma tawagar ceto da aka tura wurin ba ta samu nasara wajen ceto ta ba.

  13. 'Ba za mu zuba ido a ci gaba da kashe kiristoci a Najeriya ba'

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump na Amurka na nanata iƙirarin da ya yi cewa ''Kiristoci na fuskantar mummunan barazana a Najeriya".

    Yayin wani jawabi da ya gabatar a fadar gwamnatin ƙasar, Mista Trump ya ce Amurka ba za ta ci gaba da zura idanu ana kashe Kiristoci a Najeriya da sauran ƙasashe ba.

    ''Masu tsattsauran kishin Musulunci na ci gaba da kashe dubban Kiristoci a Najeriya, kan haka ne na sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake nuna damuwa a kansu''

    ''A shirye muke don kare ƴan'uwanmu Kiristoci a faɗin duniya'', in ji Trump.

    Shugaban na Amurka ya ce a yanzu haka ya umarci Majalisar Wakilan Amurka ta gaggauta binciken wannan lamari tare da kawo masa rahoto cikin gaggawa.

  14. Yadda na tsinci kaina a fim - Hassana ta Zaɓi Biyu

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallaon bidiyon

    A wannan makon muna kawo muku Hassana Ibrahim Rano wadda jaruma ce a fim ɗin Zaɓi Biyu mai dogon zango a kafar Arewa24.

    Ita ce jaruma ta farko a fim ɗin da ke bayyana a shirin namu na ..Daga Bakin Mai Ita.

    Hassana Ibrahim Rano wadda matashiya ce mai ƙarancin shekaru ta ce fim ɗin Zaɓi Biyu shi ne na farko da ta fara yi a rayuwarta.

    "Ni ban taɓa yin fim ba a rayuwata amma dai ina da sha'awar yi. Rannan kawai sai ga sanarwar ana neman mutanen da za a yi wa 'audition'. Yayata ce ma ta faɗa min kuma na nema. Allah ya sa aka dace."

    Dangane da matsalolin da ƴan fim ke fuskanta a gidajensu sakamakon irin kallon da ake yi wa ƴan fim, Hassana ta ce "da farko dai an samu ƴar matsala amma daga baya komai ya daidaita."

    Hassana wadda ƴar asalin jihar Kano ce ta yi firamare da sakandare da diploma sannan kuma yanzu tana yin babbar diploma duka a birnin Kano, ta ce a yanzu haka wani lokacin idan za ta fita waje sai ta yi amfani da takunkumin fuska saboda ka da jama'a su gane ta.

  15. 'Za mu tsananta hare-hare ta sama domin kakkaɓe ƴanbindiga'

    Babban hafsan sojin sama

    Asalin hoton, NAF

    Babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya bayar da umarni ga kwamandojin da ke lura da jiragen yaƙi su tsananta hare-hare kan maɓoyar ƴanbindiga a ƙasar.

    Aneke ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron da ya jagoranta tsakanin manyan kwamandojin da ke jagorantar rundunonin da ke yaƙi da ƴanbindiga a ƙasar

    Taron ya tattauna sabbin dabarun da rundunar za ta ɓullo da su wajen kai hare-hare kan maɓaiyar ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

    Sanarwar bayan da taron da rundunar sojin saman ta fitar, ta ce a ganawar manyan dakarun an ɓullo da dabarun haɗin gwiwa tsakanin rundunar sojin saman da sauran rundunonin tsaron.

    Matakin na zuwa ne mako guda bayan da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabbin shugabannin rundunonin sojin ƙasar.

  16. Amnesty ta zargi Tunisiya da take haƙƙin ƴan cirani

    Ƙungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta zargi Tunisiya da take haƙƙin ɗan'adam kan ƴan cirani ciki har da fyade da kuma azabtarwa.

    Cikin wani sabin rahoton da ƙungiyar ta fitar ta ce a yanzu an bayyana tsarin kula da ƴan cirani da kuma masu neman mafaka na Tunisiya a matsayin wanda ake nuna wariyar launin fata saboda ba a daraja da mutunta da ma kare martabatar mutane musamman baƙaƙen fata.

    Dubban mutane ne ke bi ta ƙasar domin shiga Turai a kowacce shekara.

    Amnesty ta ce mutanen da ke bi ta kasar na fuskantar cin zarafi kamar duka da fyade da sauransu.

  17. 'Gwamnatin Najeriya na tattaunawa da Amurka kan zargin Trump'

    Ministan yaɗa labaran Najeriya

    Asalin hoton, Mohammed Idris/X

    Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da hukumomin Amurka, don fahimtar juna game da zargin Trump na yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.

    A baya-bayan nan ne shugaban na Amurka ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, matuƙar ba ta tashi tsaye wajen daƙile abin da ya kira kashe Kiristoci a ƙasar ba.

    Ministan yaɗa labaran ƙasar, Muhammad Idris, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Najeriya ba ta son yin cece-kuce da Amurka da ma kowace ƙasa.

    ''Mu mun sani muna da ƙalubalen tsaro a ƙasarmu, amma gwamnatinmu na yin duk mai yiwa domin magance shi'', in ji shi.

    Ministan yaɗa labaran ya kuma ce iƙirarin na Shugaba Trump ya ba su mamaki.

    ''Waɗannan Kiristoci duka muna zaune da su a matsayin ƴan'uwan juna, kuma kundin tsarin mulkin Najeriya bai wa kowane ɗan ƙasa ƴancin yin addininsa'', kamar yadda ya bayyana.

    Ministan ya kuma ce a gwamnatin ƙasar na tattauanawa da Amurka, domin lalubo hanyar magance matsalar.

    ''A gwamnatance akwai hanyoyi da yawa da ake magana da mutanen nan, kuma ina tabbatar wa al'umma cewa za shawo kan wanna matsalar da yardar Allah'', in ji shi.

    Sai dai ministan ya kore batun cewa Trump zai gana da Tinubu kan wannan batu.

    ''Kawo yanzu dai babu wani abu makamancin haka, ama ida suna son ganawa babu abin da zai hana, tun da su biyun duka shuagabnnin ƙasashe ne, amma a yanzu ba a tsaida rana ko lokacin gudanar da hakan ba'', in ji shi.

  18. Abubuwan da suka kamata ku sani kan zaɓen gwamnan Anambra

    Wasu daga cikin ƴan takarar

    Asalin hoton, Soludo/Ukachukwu/Ezenwafor/Moghalu/Facebook

    A ranar Asabar mai zuwa ne za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya.

    Mutum 16 ne za su fafata a zaɓen ciki har da gwamnan jihar na yanzu, Chukwuma Soludo - tsohon gwamnan Babban Bankin ƙasar.

    Gwamnan jihar - wanda ɗan jam'iyyar AFGA ne na neman wa'adin mulki na biyu.

    Mutane da yawa na sa ido sosai kan abin da ke faruwa a jihar.

    Yayin da ranar zaɓe ke ƙaratowa, ga wasu muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da zaɓen.

    Latsa nan domin karanta cikakken labar

  19. ƙungiyoyin da ke rabon abinci a Sudan za su dakatar da aiki

    Wani sabon rahoto ya ce ayyukan ƙungiyoyin sa kai da ke rabon abinci a Sudan na dab da tsayawa.

    Ƙungiyoyin sun kasance masu matuƙar amfani ga miliyoyin ƴan Sudan saboda taimakon da suke yi musu.

    To sai dai ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke rabon abinci ta ce rashin kula da ƙarancin kayayyaki da kuma samun jami'an da za su riƙa aiki a ƙungiyoyin na daga cikin abubuwan da yawa daga cikin ƙungiyoyin ke fuskanta har suke neman dakatar da ayyukansu.

    A cikin El Fasher wanda mayaƙan suka ƙwace a kwanannan, ƙungiyoyin da ke rabon abincin sun kasance su ne hanyoyin da mutane ke samun abinci a lokacin da aka yi wa birnin ƙawanya tsawon watanni 18.

  20. Ana shirin rage yawan jiragen da ke tashi a Amurka

    jirgi

    Asalin hoton, EPA

    Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta tarayya a Amurkan ta ce za ta fara rage yawan jiragen da ke tashi a ranar Jumma'a a wani mataki na ci gaba da rage ayyukan gwamnati da ake yi a ƙasar.

    Hukumar ta ce za ta rage cunkoson jirage da ake samu a sararin samaniya da kashi 10 cikin 100 domin tabbatar da tsaron lafiyar mutane.

    Masu kula da zirga-zirgar jiragen saman sun ce suna aiki tuƙuru kuma tsawon wata guda kenan ba a biya su albashi ba sannan kuma akwai da yawa daga cikinsu da suka kwanta rashin lafiya.