Yadda na tsinci kaina a fim - Hassana ta fim ɗin Zaɓi Biyu
A wannan makon muna kawo muku Hassana Ibrahim Rano wadda jaruma ce a fim ɗin Zaɓi Biyu mai dogon zango a kafar Arewa24.
Ita ce jaruma ta farko a fim ɗin da ke bayyana a shirin namu na ..Daga Bakin Mai Ita.
Hassana Ibrahim Rano wadda matashiya ce mai ƙarancin shekaru ta ce fim ɗin Zaɓi Biyu shi ne na farko da ta fara yi a rayuwarta.
"Ni ban taɓa yin fim ba a rayuwata amma dai ina da sha'awar yi. Rannan kawai sai ga sanarwar ana neman mutanen da za a yi wa 'audition'. Yayata ce ma ta faɗa min kuma na nema. Allah ya sa aka dace."
Dangane da matsalolin da ƴan fim ke fuskanta a gidajensu sakamakon irin kallon da ake yi wa ƴan fim, Hassana ta ce "da farko dai an samu ƴar matsala amma daga baya komai ya daidaita."
Hassana wadda ƴar asalin jihar Kano ce ta yi firamare da sakandare da diploma sannan kuma yanzu tana yin babbar diploma duka a birnin Kano, ta ce a yanzu haka wani lokacin idan za ta fita waje sai ta yi amfani da takunkumin fuska saboda ka da jama'a su gane ta.



