Amurka ta ce ta kwashe jami'an ofishin jadancinta daga Haiti, a daidai lokacin da ayyukan ƴan daba ke ci gaba da karuwa a ƙasar.
Amurkar ta kuma ce ta tsaurara matakan tsaro a ofishin jakadancinta da ke Port-au-Prince, babban birnin ƙasar ta Haiti.
Hakan ya biyo bayan hare-haren da ƴan dabar suka kai filayen jirgin sama, ofisoshin ƴansanda da kuma gidajen yari a wannan mako.
Sun ce suna son a tsige Firaiministan ƙasar.
An tsawaita dokar ta-ɓaci ta kwanaki uku da aka ayya a faɗin ƙasar zuwa wata ɗaya.
"Ƙaruwar hare-haren ƴan daba a makwabta kusa da ofishin jadakancin Amurka da kuma filayen jiragen sama, sun janyo ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ɗaukar matakin kwashe jami'anta," kamar yadda ofishin ya wallafa a shafukan sada zumunta.
Amurkar ta ce ofishin zai ci gaba da kasancewa a buɗe.