Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An kashe mutum uku a wani hari da Rasha ta kai Donetsk
Gwamnan Donetsk da ke Gabashin Ukraine ya ce
harsashin Rasha ya kashe wasu mutum uku.
Vadym Filashkin ya ƙara da cewar adadin waɗanda
suka jikkata sakamakon hare-haren roka da Rasha ta kai a rukunin gidajen Myrnograd ya
ƙaru zuwa mutum 12, don haka ya yi kira ga mutane su bar yankin.
Ma'aikatar Tsaron
Rasha ta sanar da nasarar kakkaɓo wasu jirage marasa matuƙa biyu a yankin
Novgorod da ke Kudu masi gabashin St Petersburg.
Dubban mutane a Netherlands sun yi zanga-zanga kan ziyarar shugaban Isra'ila
Asalin hoton, Reuters
Dubban mutane a Netherlands sun yi zanga-zanga kan ziyarar da shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya kai ƙasar.
Masu zanga-zangar suna kuma adawa da kasancewar wani mutum-mutumi na Isra'ila a Gaza.
Isaac Herzog ya kai ziyara Netherlands ne domin halartar bikin sake buɗe wani gidan tarihi.
Wasu daga cikin mutanen da ke adawa da ziyarar shugaban Isra'ilar sun kasance Yahudawa.
Sun yi ta rera wakoki da ke zargin shugaban da aikata kisan kare dangi. Wani zargi da Isra'ila ta musanta.
Mr Herzog ya yai gargaɗi kan ƙaruwar musgunawa da ake yi wa Yahudawa.
Ya yi kira da a saki Yahudawan da Hamas ta yi garkuwa da su.
Yadda ake shirye-shiryen shiga watan Ramadan a sassan duniya
Al'ummar Musulmi a faɗin duniya na ci gaba da shirye-shiryen shiga watan Ramadan.
Zirin Gaza ma ba a barta a baya a shirye-shiryen.
Tuni dai aka sanar da ganin watan azumin Ramadan a Saudiyya.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yadda birnin Cologne na Jamus ke shirin shiga watan azumi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Musulmi a Gaza sun fara shirin marabtar watan Ramadan, duk da irin yaƙi da ake gwabza wa a can
Asalin hoton, Haramain Sharifain
Bayanan hoto, Shirye-shiryen azumi a Saudiyya
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Nan al'ummar Musulmi ne a Tehran, babban birnin Iran, ke shirye-shiryen shiga watan azumi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Haka ma a can Turkiyya, shirye-shirye sun yi nisa wajen tarbar watan azumi
Muna kira ga Isra'ila ta dakatar da laifukan da take aikatawa a Gaza - Saudiyya
Asalin hoton, AFP
Ƙasar Saudiyya ta yi kira ga al'ummomin ƙasashen waje da su ɗauki mataki kan Isra'ila wajen ganin ta dakatar da "munanan laifuka" da take aikatawa kan Falasɗinawa a Gaza.
Gargaɗin wanda ya fito daga Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, wanda kuma wani jami'in gwamnatin ƙasar ya fitar, ya buƙaci gwamnatoci da su samar da hanyoyin kai agaji Gaza cikin sauki.
Ana ci gaba da kokari wajen ganin ƙarin agaji ya kai zuwa Gaza, sai dai hakan ya samu cikas ganin cewa Isra'ila na ci gaba da lugudan wuta, kuma fatan tsagaita wuta da ake da ita na ƙara raguwa.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake kai agaji Gaza, kuma ana sa ran jirgin ruwa ɗauke da tan 200 na kayan abinci zai bar Cyprus zuwa Gaza a ranar Lahadi.
Amurka ta kwashe jami'an ofishin jakadancinta a Haiti kan rikicin ƴan daba
Asalin hoton, Reuters
Amurka ta ce ta kwashe jami'an ofishin jadancinta daga Haiti, a daidai lokacin da ayyukan ƴan daba ke ci gaba da karuwa a ƙasar.
Amurkar ta kuma ce ta tsaurara matakan tsaro a ofishin jakadancinta da ke Port-au-Prince, babban birnin ƙasar ta Haiti.
Hakan ya biyo bayan hare-haren da ƴan dabar suka kai filayen jirgin sama, ofisoshin ƴansanda da kuma gidajen yari a wannan mako.
Sun ce suna son a tsige Firaiministan ƙasar.
An tsawaita dokar ta-ɓaci ta kwanaki uku da aka ayya a faɗin ƙasar zuwa wata ɗaya.
"Ƙaruwar hare-haren ƴan daba a makwabta kusa da ofishin jadakancin Amurka da kuma filayen jiragen sama, sun janyo ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ɗaukar matakin kwashe jami'anta," kamar yadda ofishin ya wallafa a shafukan sada zumunta.
Amurkar ta ce ofishin zai ci gaba da kasancewa a buɗe.
Sojojin Najeriya sun kashe ƴan IPOB 20, sun tarwatsa sansaninsu a Imo
Asalin hoton, Nigerian Army/X
Dakarun sojin Najeriya sun ce sun kashe mambobin ƙungiyar ƴan awaren Biafra guda 20, a wani samame da suka kai maɓuyarsu da ke karamar hukumar Orsu na jihar Imo.
Da yake tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa yau Lahadi, darektan yaɗa labarai na sojojin Najeriya, Manjo-Janar Edward Buba, ya ce sojojin sun kuma tarwatsa sansanonin ƴan ƙungiyar kusan 50 a cikin wani daji.
"Dakarun sun kuma tarwatsa wani wurin bauta na ƴan awaren ta Biafra, da ofishinsu da kuma hedkwatar manyan kwamandojinsu," in ji sanarwar.
Janar Buba ya ce sansanonin ƴan ƙungiyar da ke cikin dajin yana ɗauke da isashen wutar lantarki, inda ya ce suna kuma amfani da wurin wajen kiwon dabbobi da kuma gonaki waɗanda suke amfani da su wajen yi rayuwa.
Samamen da sojojin suka kai ranar 7 ga watan Maris, ya kuma gano abubuwan fashewa da dama kan hanyar da ta kai sansanin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya
Asalin hoton, Getty Images
Kasar Saudiyya ta bayar da sanarwar ganin watan Azumin Ramadana.
Shafin X na Masallatan Harami biyu masu daraja ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa.
Ganin watan ya sa gobe Litinin za ta zama 1 ga watan Ramadan na shekarar 1445, wanda ya zo daidai da 11 ga watan Maris ɗin 2024.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Hukumar Masallatan ta sanar da cewa a daren yau ne za a fara gabatar da Sallar Asham, inda Sheikh Sudais da Sheikh Badr Al Turki da kuma Al Waleed Al Shamsaan za su jagorance ta a Masallacin Harami na Makkah, yayin da Sheikh Muhammad Barhaji da Abdul Muhsin Al Qasim za su jagoranci sallar a Masallacin Manzon Allah SAW na Madina.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Ana fargabar gini mai hawa biyar ya ɗanne mutane da dama a Anambra
Asalin hoton, Getty Images
Ana fargabar cewa wani gini mai hawa biyar ya rufta tare da danne mutane da dama a birnin Onitsha, na jihar Anambra.
Rahotanni sun bayyana cewa ginin, wanda ba a kammala gina shi ba, ya rufta a safiyar yau Lahadi lokacin da masu aikin gini ke hawa na karshe.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa tuni aka tura motar Katafila zuwa wajen domin fara aikin fitar da mutanen da ake kyautata zaton gini ya danne su.
Zuwa yanzu dai ba a san musabbabin ruftawar benen ba, sai dai wani ganau kusa da yankin ya bayyana cewa an ceto wani mutum guda yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
NDLEA ta kama kwaya da aka ɓoye cikin injin mota
Asalin hoton, NDLEA
Jami’an hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Najeriya sun kama wasu tarin ƙwayoyi da aka ɓoye cikin inji wata motar bas a kan babban titin Gbongan zuwa Ibadan.
Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran hukumar Femi Babafemi ya fitar, ya ce hukumar ta kuma kama wasu mutum biyu da ta ce sun manyanta bisa zargin safarar ƙwaya a ƙasar.
Babafemi ya kuma ce hukumar ta NDLEA ta kama wata mata mai shekara 26 da ake zargi da safarar abun maye a kwalabe a lokacin samamen da jami'an hukumar suka kai maɓoyarta a jihar Osun.
Sanarwar ta ce ta kama aƙalla lita 16.5 na ruwan kwalaben da kuma tabar wiwi a lokacin samamen.
Asalin hoton, NDLEA
Somaliya ta zartar da hukuncin kisa kan mutumin da ya kashe mahaifiyarsa
Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a Kismayo da ke Somliya ta jagoranci aiwatar da hukuncin kisa kan wani mutum da a baya aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai.
A ranar 16 ga watan Oktoban bara ne kotun ta samu Hassan Abdullahi da laifin kashe mahaifiyarsa mai suna Halima Mohammed Omar ranar 11 ga watan Yunin bara.
Kafin aiwatar da hukuncin kisan, baban alƙalin yankin Jubbaland, Nuradidin Mohamed Khalif, ya yi bayanin yadda aka sauya hukuncin farkon.
Israi'ila ta tsaurara tsaro a Birnin Ƙudus gabanin fara azumin Ramadan
Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta ƙara tsaurara matakan tsaro a Birnin Ƙudus gabanin fara azumin watan Ramadan.
An girke dubban 'yansanda a tsohon birnin, inda ake sa ran dubban musulmai za su riƙa halartar masallcin Al-Aqsa (masallaci a uku mafi daraja a duniya a wajen musulmai) a kowace rana.
Yayin da ake ci gaba da gwambza yaƙi a Gaza, ƙungiyar Hamas ta yi kira ga Falasɗinawa su ƙara ƙaimi wajen halartar masallacin.
Masallacin ya kasance wani kafar rikici tsakanin musulmai da Yahudawa.
Kawo yanzu babau wani sauran fata na tsagaita wuta cikin watamn azumin, inda Isra'ila ta zargi Hamas da ɗaukar tsattsauran matsayi a yarjejeniyar.
Amsoshin Takardunku
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Damisar da aka kai Indiya daga Afirka ta Kudu ta haifi 'ya'ya biyar
Asalin hoton, byadavbjp
Damisar da aka kai Indiya daga Afirka ta Kudu, mai suna Gamini,ta haifi 'ya'ya biyar a gandun dajin Kuno da ke jihar Madhya Pradesh.
Ministan kula da gandun daji na ƙasar, Bhupendra Yadav ne ya tabbatar da haihuwar damisar.
Ya ƙara da cewa a yanzu adadin 'yan'yan damisar da aka haifa a ƙasar sun kai 13.
A yanzu gandun dajin Kuno da na damisa da yawansu ya kai 26 idan aka haɗa da waɗannan biyar da aka haifa yanzu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
RSF ta yi maraba da kiran MDD na tsagaita wuta a watan Ramadan
Asalin hoton, Reuters
Dakarun RSF a Sudan sun yi maraba da kiran Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita wuta a yaƙin da ake yi a ƙasar, a lokacin watan azumin Ramadan.
Cikin wata sanarwa da RSF din ta fitar, rundunar ta bayyana fatanta kan matakin da kwamitin tsaro na MDD ya ɗauka zai taimaka wajen rage wahalhalun da 'yan ƙasar ke fuskanta, tare da bayar da damar kai kayan agaji wuraren da ake buƙatarsu.
Mayaƙana na RSF sun ce suna fatan dakatar da wutar a watan azumin, zai taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin baki-ɗaya.
A ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2023 ne yaƙi ya ɓarke tsakani sojojin gwamnatin Sudan da dakarun RSF.
Rikicin da MDD ta ce ya jefa kusan mutum miliyan 25, kimanin rabin al'ummar ƙasar cikin halin buƙatar tallafi, tare da raba kusan mutum miliyan takwas da muhallansu.
Tinubu ya umarci Kwastam ta mayar da kayan abincin da ta kwace wa mutane
Asalin hoton, NIGERIA CUSTOMS/X
Babban Kwanturan Hukumar Kwastam ta Najeriya, Bashir Adewale Adeniyi ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu ya umarci hukumar ta mayar da duka abinci dangin tsaba da ta ƙwace daga wajen mutane domin sayar da su a kasuwanni.
Cikin wata sanarwa da hukumar Kwastam ɗin ta fitar a shafinta na X, ta ce mista Adeniyi ya bayyana hakan ne lokacin wata ziyara da ya kai kan iyakar Kwangwalam da ke ƙaramar hukumar Maiadua a jihar Katsina inda ya gana da masu ruwa da tsaki.
Shugaban Kwastam ɗin ya ce umarnin shugaba Tinubun wata alama ce da ke nuna burin shugaban ƙasar na tabbatar da al'ummar ƙasar sun wadata da abinci ta yadda farashinsa zai sauka a kasuwannin ƙasar.
Ya ƙara da cewa sharaɗin mayar da kayan abincin hannun mutanen da aka ƙwace musun, shi ne za su sayar da shi a kasuwannin Najeriya.
Mista Adeniyi ya kuma ce dole ne a samu dangantakar alaƙa tsakanin jami'an tsaro da ci gaban tattalin arziki, yana mai cewa idan babu zaman lafiya da tsaro kasuwanci ba zai inganta ba.
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga uku a dajin Sambisa
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya da ke aikin yaƙi da 'yan bindiga a yankin arewa maso gabashin Najeriya ta ce ta kashe 'yan bindiga uku tare da lalata sansanin 'yan bindigar a dajin Sambisa.
Cikin wata sanarwar da daraktan yaɗa labaran rundunar sojin ƙasa na Najeriya Onyema Nwachuku ya fitar, ya ce cikin waɗanda sojoin suka kashe har da ɗan ƙunar-baƙin-wake, tare da ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 biyu.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a wani samamen na daban da sojojin suka kai sansanin 'yan bindigar - da ke yankin Buluwa na ƙaramar hukumar Kukawa - sun kashe wani ɗan bingida guda tare da ƙwato bindiga guda ƙirar AK-47 da harsasai 14 da babur guda ɗaya da kayan abinci da sauran kayayyaki.
A baya-bayan dai matsalar tsaro na ci gaba da addabar wasu sassan arewacin Najeriya, inda a karhsne makon da ya gabata wasu da ake kyautata zato mayaƙan Boko Haram ne suka sace wasu 'yan gudun hijira fiye da 100 a jihar Borno.
Haka ma a ranar Alhamis ɗin da ta gabata wasu 'yan bindiga suka sace daliban makarantar furamare da na ƙaramar sakandiren Kuriga a jihar Kaduna.
Daliban Kuriga 28 sun kuɓuta daga hannun 'yan bindiga - Uba sani
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce dalibai 28 daga cikin daliban makarantar Kuriga fiye da 280 da 'yan bindiga suka sace sun kbuta daga hannun maharan.
Gwamnan ya kuma ce samar da ƴan sandan jihohi ne zai magance matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Hikayata: Labarin Cizon Yatsa
A ci gaba da kawo muku jerin labarai 12 da alƙalan gasar Hikataya ta 2023 suka ce sun cancani yabo, a yau mun kawo labari na ƙarshe cikin jerin, mai suna Cizon Yatsa.
Labari ne da Aisha Adam, mazauniyar Kadawa, Layin Masjidul Qur’an, Bayan Sabuwar Tasha, Rijiyar Zaki, a birnin Kano, ta rubuta.
Labari ne na wata matar aure da ta tsinci Talatarta a Laraba, bayan da ta biye wa son zuciya da ruɗin ƙawa, ta yi watsi da aurenta da 'ya'yanta, ta kuma shiga neman duniya, ƙarshe dai duniyar ba ta samu ba, sai dai tarin nadama.
Nabeela Mukhtar Uba ce ta karanta labarin
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron labarin