Ƴan sandan Najeriya sun tarwatsa gugun ƴan bindiga a jihar Anambra
Jami’an tsaro a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta-da-kayar-baya a yankin Achalla da ke karamar hukumar Awka ta arewa.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga ya fitar, ya ce sun kwato motoci biyar da miyagun makamai da suka gano a maoyar ‘yan ta’addan.
Ikenga ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun kawo cikas a kasuwar Achalla a ranar Litinin ɗin da ta gabata, lamarin da ya tilasta wa ‘yan kasuwar su zauna a gida.
''Hakan ya jawo hankalin jami’an tsaro a jihar wanda hakan ya sanya rundunar ‘yan sandan jihar ta yanke shawarar maida masu martani da sanyin safiyar ranar Litinin,'' in ji Ikenga.
Ya ce sakamakon nasarar da aka samu ya kai ga kwato wasu manyan motoci guda biyar da aka kwace a baya. Haka kuma an samu harsashin bindiga sama da 300 na bindigar Ak-47.”
Dukkan ma’aikatan da suka fito daga ayyuka daban-daban sun koma sansaninsu lafiya, a cewar kakakin ƴan sandan.