Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Ahmad Tijjani Bawage and Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Ƴan sandan Najeriya sun tarwatsa gugun ƴan bindiga a jihar Anambra

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Jami’an tsaro a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta-da-kayar-baya a yankin Achalla da ke karamar hukumar Awka ta arewa.

    A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga ya fitar, ya ce sun kwato motoci biyar da miyagun makamai da suka gano a maoyar ‘yan ta’addan.

    Ikenga ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun kawo cikas a kasuwar Achalla a ranar Litinin ɗin da ta gabata, lamarin da ya tilasta wa ‘yan kasuwar su zauna a gida.

    ''Hakan ya jawo hankalin jami’an tsaro a jihar wanda hakan ya sanya rundunar ‘yan sandan jihar ta yanke shawarar maida masu martani da sanyin safiyar ranar Litinin,'' in ji Ikenga.

    Ya ce sakamakon nasarar da aka samu ya kai ga kwato wasu manyan motoci guda biyar da aka kwace a baya. Haka kuma an samu harsashin bindiga sama da 300 na bindigar Ak-47.”

    Dukkan ma’aikatan da suka fito daga ayyuka daban-daban sun koma sansaninsu lafiya, a cewar kakakin ƴan sandan.

  2. Wata mata ta haihu a tashar mota a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Wata mata ta haihu a tashar mota da ke birnin Legas a Najeriya.

    Hukumar agajin gaggawa ta sanar cewa matar da ba a bayyana sunanta ba tana jiran shiga motar bas ne a tashar Onipanu Bus Stop a lokacin da ba zato ba tsammani ta shiga naƙuda a ranar Litinin.

    Mata ƴan kasuwa ne suka taimaka ma ta, yayin da masu ba da agajin gaggawa suka garzaya wurin.

    Hukumar agajin gaggawa ta ƙara da cewa, ta haifi ɗa namiji, kuma tuni aka kai mahaifiyar da yaron asibiti. domin duba lafiyarsu

    Babu wani ƙarin bayani da aka bayar game da su baya ga haka, amma 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta na ta wallafa sakonnin taya murna har ma da shawaran sunayen da za a raɗawa jaririn.

  3. Hukumar kwastam ta Najeriya za ta raba kayan abincin da aka kama a faɗin ƙasar

    ...

    Asalin hoton, NIGERIA CUSTOM SERVICE

    Hukumar Kwastam ta Najeriya, NCS, ta ce tana shirin raba wasu kayayyakin abincin da aka kama a faɗin ƙasar, yayin da ake ci gaba da fama da matsalar karancin abinci a kasar.

    A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar, CSC Abdullahi Maiwada, za a raba kayan abincin ne bayan an tabbatar da cewa mutane za su iya amfani da su.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an ɗauki matakin ne "domin rage wahalhalun da 'yan Najeriya ke fuskanta da kuma inganta hanyoyin samun kayan abinci, hukumar kwastam za ta taimaka wajen raba kayan abincin da hukumar ta kama kai tsaye.

    Sanarwar ta ƙara da cewa “Za a sanar da tsarin da za a yi amfani da shi a ofisoshin hukumar da ke fadin kasar, tare da jajircewa wajen tabbatar da adalci. Mun sha alwashin cewa za a gudanar da wannan aikin domin tabbatar da cewa kayayyakin sun kai ga waɗanda suka fi bukata.”

  4. Amurka na shirin yin kiran tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta gabatar da daftarin ƙuduri a kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ya buƙaci a tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza. Ta kuma gargadi Isra'ila game da kai mamaya birnin Rafah.

    A baya dai Amurka ta kaucewa amfani da kalmar "tsagaita wuta" a lokacin kuri'un da Majalisar Dinkin Duniya ta kaɗa kan yaƙin, amma shugaba Joe Biden ya yi irin waɗannan kalaman.

    Wannan dai shi ne karon farko da Amurka ta yi kira da a tsagaita bude wuta na wucin gadi a Gaza a Majalisar Dinkin Duniya, bayan da ta ki amincewa da ƙudurorin da suka gabata.

    Daftarin na Amurka ya kuma bayyana cewa, wani gagarumin farmakin ƙasa da za a kai a Rafah zai haifar da mummunar illa ga fararen hula da kuma ƙara yawan ƴan gudun hijira.

    Za a fara tattaunawa kan daftarin na Amurka a cikin wannan makon, amma ba a bayyana yaushe za a kaɗa ƙuri'a a kan ƙudurin ba.

  5. Ƙungiyar NARTO ta janye shirin shiga yajin aiki

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar masu motocin sufuri ta Narto ta sanar da janye shirin shiga yajin aiki da ta yi niyyar yi.

    Hakan ya biyo bayan wani zama da suka yi da gwamnatin tarayya da kuma masu ruwa da tsaki a ranar Litinin bayan da direbobin tankokin mai suka dakatar da aiki da kuma daina ɗakon man fetur.

    Karamin ministan man fetur Ekperikpe Ekpo, ya ce an cimma yarjejeniya kan buƙatun mambobin ƙungiyar ta Narto.

    Tun da farko dai masu motocin sufurin sun yi barazanar dakatar da zirga-zirga a faɗin ƙasar fara wa daga jiya Litinin kan tsadar dizel, wadda suke amfani da shi wajen yin zirga-zirga.

    Ministan ya ce hukumomin gwamnati za su ci gaba da tattaunawa da mambobin ƙungiyar, inda ya ce ba za a bari lamarin ya taɓarɓare ba.

  6. Putin ya bai wa Kim Jong Un Kyautar motar alfarma

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya baiwa shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un wata motar alfarma ƙirar Aurus.

    Kafofin yaɗa labaran gwamnatin Pyongyang sun ce a ranar Lahadin da ta gabata ne aka kai wa manyan mukarraban Mr Kim motar.

    Mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov ya tabbatar da kyautar, yana mai cewa motar alfarma ce irin wadda Mista Putin ke amfani da ita.

    Bayanai sun nuna cewa Kim Jong-un yana sha'awar motoci kuma yana da tarin motocin alfarma na ƙasashen waje.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙasashen biyu sun ƙulla alaƙa tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.Ana kyautata zaton Koriya ta Arewa na baiwa Rasha makamai masu linzami da rokoki, duk da takunkuman da ƙasashen duniya suka ƙaƙabawa ƙasashen biyu.Mista Putin ya karɓi baƙuncin Mista Kim a watan Satumban da ya gabata, a ziyararsa ta farko zuwa ƙasar waje cikin shekaru huɗu.

  7. Ma'aikatar ilimin jihar Kano za ta fara hukunta yaran da ba sa zuwa makaranta

    Iyaye sun fara tofa albarkacin bakinsu game da yunƙurin da hukummomi ke yi na hukunta iyaye da yaran da basa zuwa makaranta kuma suke gararamba a kwararo a jihar Kano.

    Ma’aikatar ilimi ta jihar ta ce za ta ɗauki matakin hukunta ɗaliban ne, kasancewar gwamnati ta samar da tsarin ilimi dole kuma kyauta.

    Sai dai iyaye da dama na ganin ya kamata gwamnati ta fara kyautata ilimi a gani a kasa kafin a dauki irin wannan mataki.

    Haruna Doguwa, kwamishinan ilimi na jihar Kano ya ce ɗaya daga cikin matakin da za a ɗauka wajen hukunta yaran da ba sa zuwa makaranta shine bayar da kashadi na farko, idan suka sake , sai a bayar da kashaidi na biyu, bayan wannan kuma suka sake aikata laifin, sai dai a dakatar da su.

    Ga ƙarin bayani a cikin wannan rahoton.

    Bayanan sautiLatsa lasifikar sama domin sauraron rahoton
  8. Wace ce Murja Ibrahim Kunya?

  9. Yawan marasa aikin yi ya ƙaru a Najeriya bayan cire tallafin man fetur

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Adadin marasa aikin yi a Najeriya ya karu zuwa kashi biyar cikin 100 a rubu'i na uku na shekarar 2023, daidai lokacin da ake fama da matsalar tsadar rayuwa bayan da gwamnati ta cire tallafin man fetur.

    Shugaba Bola Tinubu ya kare manyan sauye-sauyen da ya yi guda biyu da suka haɗa da cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa da tantance darajar naira, inda ya ce duk da cewa hakan zai haifar da wahalhalu na kankanin lokaci, suna da muhimmanci wajen samar da masu zuba hannun jari da habaka kuɗaɗen gwamnati.

    Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta ce adadin marasa aiki ya tashi daga kashi 4.2 cikin 100 a cikin kwata na baya.

    Adadin marasa aikin yi a tsakanin matasa masu shekaru 15-24 ya tashi zuwa kaso 8.6 daga kaso 7.2.

    Rashin aikin yi a cikin birane shi ma ya ƙaru kaɗan zuwa kaso 6 daga kaso 5.9 a rubu'in da ya gabata.

    Najeriya wadda ita ce ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka mai sama da mutane miliyan 200, ta yi fama da marasa aikin yi tsawon shekaru da dama, sakamakon ƙaruwar yawan al'umma da ya zarce ci gaban tattalin arzikin ƙsar.

    Adadin ayyukan yi na yau da kullun, wanda ke auna yawan ma’aikata a cikin tattalin arziki ya sami canji kaɗan da kaso 92.3, a cewar NBS, aikin ma’aikata shi ma ya faɗi kaɗan zuwa kaso 79.5 daga kaso 80.4 a cikin kwata na biyu.

  10. An rufe makarantu a Habasha saboda matsalar tsaro

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Sama da makarantu 3,000 ne aka rufe saboda barazanar tsaro a rikicin yankin Amhara da ke arewa maso yammacin kasar Habasha, in ji ofishin ilimi na yankin.

    Rikici ya barke a cikin watan Afrilun bara tsakanin dakarun gwamnati da wata kungiyar ‘yan bindiga da aka fi sani da Fano, kan matakin rusa wata kungiyar ‘yan ta’adda da ke da alaka da kabilanci tare da shigar da mambobinta cikin sauran jami’an tsaron yankin da na kasa.

    Yayin da dakarun gwamnati suka kakkabe iko da yankunan birane, ana ci gaba da gwabza fada a kauyuka da kuma yankunan da ke kusa da tsaunuka a yankin na biyu mafi yawan jama'a a kasar Habasha.

    Mataimakin shugaban hukumar ilimi ta yankin, MekuanintAdeme ya ce duk da wadannan ƙalubale ana kokarin fara karatu a makarantu a yankunan da akwai kwanciyar hankali.

    A farkon wannan wata ne majalisar dokokin Habasha ta amince da kudirin tsawaita dokar ta baci na tsawon wasu watanni hudu da ke nuni da sauyin yanayi a yankin.

  11. Ƙudirin ƙirƙiro ƴansandan jihohi ya tsalake karatu na biyu a zauren majalisa

    ...

    Asalin hoton, other

    Ƙudirin ƙirƙiro da ƴansandan jihohi a Najeriya ya tsalake karatu na biyu a zauren majalisar wakilai.

    Ƙudirin wanda ƴan majalisar 13 suka ɗauki gabatar, ya samu goyon bayan mafi rinjayen ƴan majalisar waɗanda suka yi imanin cewa gwamnonin jihohi ya kamata su mayar da hankalinsu ga halin da ake ciki na rashin tsaro a fadin kasar.

    A makon da ya gabata, Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin jihohi 36 suka tattauna kan batun samar da ƴansandan jihohi don magance matsalolin tsaro da ke barazana ga ƙasar, waɗanda suka haɗa da satar mutane da fashi da makami da suka zama tamkar ruwan dare.

    Ƙirƙirar ƴansandan jihohi dai ta kasance batun da ya daɗe ana muhawara a kai a ƙasar.

    Gwamnonin da aka zaɓa a karkashin jam’iyyar PDP a baya-bayan nan sun sake jaddada muhimmanci ƙirƙirar ƴansandan jihohin, a matsayin mafita ga taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.

    Har ila yau, kungiyoyin siyasa da na al'umma irin su Afenifere da Ohanaeze Ndigbo da Middle Belt Forum, sun sha yin kira da a kafa ƴansandan jihohi domin magance mummunan ƙalubalen tsaro da ke addabar al’ummar Najeriya.

    Tuni dai jihohi a shiyyar Kudu-maso-Yamma sun kafa kungiyar Amotekun yayin da takwarorinsu na yankin Kudu maso Gabas suma suka ƙirƙiri jami’an tsaro da suke kira Ebube Agu. Haka kuma Benue ta kafa 'The Benue guards' kuma sun fara aiki da dai sauransu.

  12. Kenya za ta fara sanya ido kan ayyukan intanet don yaƙar ta'addanci

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar Kenya na shirin fara sanya ido kan ayyukan intanet na mutanen da ake kyautata zaton suna da hannu a aikata laifuka amma ba a tuhume su da nufin yaƙi da ta'addanci, kamar yadda jaridar The Star mai zaman kanta ta ruwaito.

    "A cikin sabbin dokokin da ma'aikatar harkokin cikin gida ta fitar, ƙasar na neman tilastawa masu samar da intanet raba irin bayanan da ake buƙata game da irin waɗannan mutane da ake zarginsu da hannu a aikata laifuka," in ji jaridar.

    "Za a buƙaci kamfanonin da ke ba da damar yin amfani da intanet su ci gaba da rikodin ayyukan masu amfani da intanet kuma za a tilasta musu su sake bayanan ga ƙasar."

    Jaridar ta kara da cewa gwamnati ta samar da ka'idoji don tunkarar laifukan da suka kunno kai, inda intanet da shafukan sada zumunta suka zama sabon filin ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

    Kenya dai na fuskantar barazana daga kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab.

  13. Ƙasar Djibouti ta ceto ma'aikatan jirgin ruwan Birtaniya da 'yan Houthi suka kai wa hari

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomi a tashar jirgin ruwan Djibouti sun kuɓutar da wasu ma'aikatan jirgin ruwan Birtaniya da ƙungiyar 'yan tawayen Houthi mai samun goyon bayan Iran suka kai wa hari, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ADI ya bayyana.

    ADI ya ce hukumomin tashar jirgin ruwan sun kai ɗauki bayan kiran wayar da suka samu daga jirgin ruwan, Rubymar, abin da ya sa aka iya kwashe. An ba da rahoton jirgin na nutsewa a tekun bahar maliya.

    Gwamnatin Djibouti ta ce ta kuɓutar da mutum 24 ciki har da yan Syria 11 sai 'yan Masar shida da Indiyawa uku da 'yan Phillipine huɗu.

    "Aikin agajin ya nuna irin rawa mai muhimmanci da tashar jirgin ruwan Djibouti ta taka wajen tabbatar da tsaron ruwa da taimaka wa jiragen da ke fuskantar haɗari. A lokacin da rikicin wani yanki ke tada ƙura a wannan yanki, Djibouti ta sake zama wani waje na tsaro da daidaito," in ji ADI.

    Ƙungiyar da ke kula da harkokin cinikiayya ta ruwa a Birtaniya ta ce an kai wa jirgin hari mil sittin daga babban birnin Djibouti.

  14. Mayaƙan Fano sun ƙwace wani babban gari a Habasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar 'yan bindiga ta Fano da ke yankin Amhara na ƙasar Habasha ta yi ikirarin cewa ta kwace wani babban gari bayan kazamin fada da sojojin ƙasar, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta Habasha (EMS) da ke Amurka ta ruwaito.

    “Mayaƙan Fano sun kai farmakin ba-zata kan jami’an tsaron da ke Wuchale tare da ƙwace garin, kamar yadda majiyar EMS ta bayyana daga yankin.

    EMS ta ce mayaƙan na Fano sun kuma ƙwace makamai iri-iri daga hannun sojojin.

    "Ko da yake an ce fadan ya lafa, sojojin sun ci gaba da luguden wuta a garin tun daga tudun Ambasel, inda suka jikkata wasu fararen hula." in ji EMS.

    Mayaƙan Fano, waɗanda ke iƙirarin fafutukar kare hakkin kabilar Amhara, sun yi ta fafatawa da sojojin gwamnatin Habasha tun a watan Afrilun 2023 bayan sun bijirewa umarnin ajiye makamai.

    • Abin da ya sa yaƙin Ethiopia ya sake zama sabo a Tigray da Amhara
    • Yaƙin Tigray: Ana zargin sojojin Eritrea da yi wa mata fyaɗe duk da yarjejeniyar zaman lafiya
  15. Kotu ta tura Murja Kunya zuwa asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa

    Murja Ibrahim Kunya

    Asalin hoton, fb/Murja Ibrahim

    Bayanan hoto, Murja Ibrahim Kunya

    Wata kotu da ke zaman ta a birnin Kano ta bayar da umarnin tura ƴar tiktok Murja Ibrahim Kunya zuwa asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiyar ƙaƙwalwarta.

    Mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Babajibo Ibrahim ne ya tabbatar wa BBC hakan bayan zaman kotun da aka yi a yau Talata.

    A hirar sa da BBC, Babjibo ya ce "yanayin da take ciki da kamannunta da kuma maganganun da take faɗa sun nuna cewa ba ta cikin hali na cikakken hankali."

    Ya ƙara da cewa "wannan ne dalilin da ya sa alƙalin ya buƙaci a tura wadda ake zargin zuwa asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa har zuwa ranar 20 ga watan biyar, 2024."

    Hukumar Hizba ta jihar Kano ce ta kama Murja Kunya tare da miƙa ta ga jami'an tsaro bisa zargin ta da laifukan da suka shafi baɗala a shafukan sada zumunta.

    Kwamandan hukumar ta Hizba a jihar, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce tuhume-tuhumen da ake yi wa Murja Kunya sun haɗa da: Razana al'umma, ayyukan baɗala, tayar da hatsaniya, tayar da hankalin al'umma, kawo ɓata-gari cikin unguwa da kuma iƙirarin cewa ita ce shugaban karuwai da ƴan kwalta.

    Batun kamawa da tura fitacciyar ƴar tiktok ɗin zuwa gidan yari ya ja hankalin al'ummar a jihar ta Kano.

    Haka nan labarin fitar da ita daga inda kotu ta tura ta, wato gidan gyaran hali shi ma ya janyo muhawara mai zafi a jihar.

    A ranar Litinin gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba ta da hannu a sakin ƴar tiktok ɗin daga gidan yari bayan umarnin da kotu ta bayar na tsare ta.

    • An tisa ƙeyar Murja Kunya da Ashiru da wasu 'yan TikTok biyu gidan yari
    • 'Yan Kannywood na mayar da martani kan hana su amfani da kayan 'yan-sanda
  16. Ecowas na tunanin yadda za a sassanta da Nijar da Mali da Burkina Faso

    ...

    Asalin hoton, Ecowas/Facebook

    Sshugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (Ecowas) na shirin tattaunawa kan sassantawa da kuma shawo kan ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da ke ƙarƙashin jagorancin mulkin soja daga ficewa daga kungiyar a yayin taron su na gaba kamar yadda gidan rediyon Faransa na RFI ya rawaito

    Ƙasashen uku sun buƙaci gaggauta ficewa daga kungiyar bayan bayyana aniyarsu ta ficewa daga kungiyar a ranar 29 ga watan Janairu.

    "Muhimmin ra'ayinmu shi ne a tuntube su don su ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar," in ji wata majiya da RFI ta ambato.

    “Don cimma wannan…tattaunawar na iya kasancewa kan takunkumin da aka kakaba wa Nijar."

    Shugabannin kasashe irin su Faure Gnassingbe na Togo suna kira da a ɗage waɗannan takunkumin," in ji RFI, inda ya kara da cewa "a halin yanzu babu tabbas".

    Rahoton na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da aka ruwaito shugaban hukumar ta Ecowas Omar Alieu Touray ya ce da wuya ƙungiyar ta bai wa ƙasashen yankin Sahel din uku damar ficewa daga kungiyar da wuri.

    • Yadda ficewa daga Ecowas zai shafi Mali da Nijar da Burkina Faso
    • Me ya rage wa Nijar, Mali da Burkina Faso bayan ficewa daga Ecowas?
  17. Yaƙin Isra'ila da Gaza: Amurka ta yi kira da a tsagaita buɗe wuta na wucin gadi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta gabatar da daftarin kuduri ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya buƙaci a tsagaita bude wuta na wucin gadi a Gaza.

    Ta kuma gargadi Isra'ila game da mamaye birnin Rafah inda Falasdinawa da dama ke neman mafaka.

    A baya dai Amurka ta kaucewa kalmar "tsagaita wuta" a lokacin kuri'un da Majalisar Dinkin Duniya ta kada kan yaƙin, amma yanzu shugaba Joe Biden ya yi irin wadannan kalamai.

    Sai dai kuma, Amurka na shirin yin watsi da wani daftarin kudiri - daga Aljeriya - wanda ya buƙaci a tsagaita bude wuta na jin kai cikin gaggawa.

    Fiye da Falasɗinawa miliyan guda da suka rasa matsugunansu, wadanda ke wakiltar kusan rabin al'ummar Gaza ne ke neman mafaka a Rafah.

    Birnin Rafah da ke kudancin ƙasar, wanda ke kan iyaka da Masar, ya kasance wurin mutane 250,000 ne kawai kafin yaƙin.

    Yawancin mutanen da suka rasa matsugunansu suna zaune ne a cikin sansanoni ko tantuna a cikin mawuyacin hali, tare da ƙarancin samun tsaftataccen ruwan sha ko abinci.

    Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da nata gargadin cewa harin da Isra'ila ke shirin kai wa a birnin na iya haifar da "bala'i da mace-macen mutane da dama".

    • Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas
    • Yadda karancin maganin kashe radadi ke jefa mutane cikin mawuyacin hali a Gaza
  18. Ƴan Najeriya sun mayar wa ɗan Tinubu martani bayan ya ce 'a yi haƙuri da halin ƙunci'

    Ɗan shugaban ƙasar Najeriya, Seyi Tinubu

    Asalin hoton, instagram/Seyi Tinubu

    Bayanan hoto, Ɗan shugaban ƙasar Najeriya, Seyi Tinubu

    Ƴan Najeriya sun yi wa ɗan shugaban ƙasar Bola Tinubu ca, bayan da ya buƙaci al'umma su ƙara haƙuri da mahaifinsa sanadiyyar halin da ƙasar ke ciki.

    Al'umma a Najeriya na cikin ƙuncin rayuwa sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi da taɓarɓarewar darajar kuɗin ƙasar, naira.

    A wani saƙo da ya wallafa ta shafinsa na instagram, Seyi Tinubu ya ce "Ba abin jin daɗi ba ne yadda mutanen Najeriya ke shan wahala kan lamarin da ya kamata a ce an wuce batun shi tun a shekarar da ta gabata.

    "Na so a ce babu waɗannan wahalhalu da ake sha."

    Ya ƙara da cewa "Sai dai wajibi ne mu jure domin jin daɗi a nan gaba."

    Bayan wanann saƙo da ya wallafa ne ƴan Najeriya da dama, musamman a shafukan sada zumunta suka mayar wa ɗan na shugaban ƙasa martani.

    Shahararren mawaƙi da ake kira Charly Boy ya wallafa a shafinsa na X cewa "Seyi Tinubu na ɗaura agogon naira miliyan 350 yayin da yake ce wa ƴan Najeriya su jure wa wahalar da ake ciki, mun ji."

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    A nasa martanin, tsohon mai magana da yawun shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, wato Reuben Abati, wanda ya wallafa a shafin X, cewa ya yi "Seyi na da ƙarfin halin da zai tsoma bakinsa a wannan batu? Yana tunanin wannan lamari ne na cikin iyali? Me ya sani game da juriya?"

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

    Seyi na daga cikin ƴaƴan shugaba Bola Ahmed Tinubu da suka fi janyo cece-ku-ce a ƙasar.

    Ko a kwanakin baya shugaban na Najeriya ya buƙaci ɗan nasa da duk wani da ba a buƙata ba da su daina shiga babban zauren taro na fadar shugaban ƙasar.

    • Ƙarin hauhawar farashin da aka daɗe ba a gani ba na gigita ƴan Najeriya
    • Wace dabara ta rage wa Tinubu game da tsadar rayuwa a Najeriya?
  19. Shugaban Senegal ya fara tattaunawa kan sabuwar ranar gudanar da zaɓe

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya fara tattauna da ƴan siyasa kan sabuwar ranar gudanar da zaɓen ƙasar, in ji jaridar Le Quotidien mai zaman kanta a yau.

    Ƙasar dai ta faɗa cikin ruɗani bayan da shugaba Sall ya ɗage zaɓen da za a yi ranar 25 ga watan Fabrairu kafin babbar kotun ƙasar ta soke matakin tare da yin kira da a gudanar da zaɓen cikin gaggawa.

    Shafin intanet na Seneweb ya ce ana sa ran shugaban na Senegal zai bayyana sabuwar rana nan ba da jimawa ba.

    A halin da ake ciki kuma, 'yar takarar shugaban kasa Rose Wardini wadda majalisar tsarin mulkin ƙasar ta wanke a watan Janairu duk da kasancewarta 'yar kasar Senegal da Faransa ta fice daga zaben, kamar yadda shafin intanet ɗin ya ruwaito.

    Batun Wardini na daga cikin batutuwan da shugaba Sall da jam'iyyar Demokradiyar Senegal (PDS) suka gabatar domin tabbatar da ɗage zaɓen har zuwa watan Disamba domin ba da damar gudanar da bincike kan tantance 'yan takarar shugaban kasa.

    Mummunar zanga-zangar da aka yi a Senegal ta sa Faransa da Tarayyar Turai da kuma ƙungiyar Ecowas ta yammacin Afirka suka buƙaci Sall da ya mutunta shawarar majalisar tare da gudanar da zaɓe cikin gaggawa.

    • Yan takara a Senegal sun buƙaci a yi zaɓe cikin mako 6
    • Ba zan yi tazarce ba - Shugaban Senegal
  20. Gwamnatin Guinea ta rusa majalisar ministocin ƙasar

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban riƙon ƙwarya na ƙasar Guinea, Mamady Doumbouya, ya kori dukkan ministocinsa, ya kuma umurce su da su miƙa fasfo dinsu, da masu gadinsu, da motocin hukuma, tare da hana su amfani da asusun ajiyarsu na banki.

    Babban sakataren fadar shugaban kasa, Birgediya Amara Camara ne ya bayyana hakan ba zato ba tsammani a wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na RTG.

    Manyan jami'ai, waɗanda aka gayyace su zuwa fadar shugaban kasar don "zaman aiki", za su karɓi ragamar tafiyar da ma'aikatun gwamnati har sai an naɗa sabuwar majalisar ministoci, in ji Brig Gen Camara.

    Ba a bayar da dalilin yanke hukuncin ba, amma an umurci kwamandojin Jandarma da ‘yan sanda da su “rufe” dukkan iyakokin ƙasar har sai an miƙa ma’aikatun gwamnati gaba daya.

    Ƙasar da ke yammacin Afirka ta kasance karkashin mulkin soja tun bayan da sojoji suka kƙwace mulki a watan Satumban 2021.

    Babbar kungiyar tattalin arziki da siyasa ta yankin, Ecowas, ta dade tana matsawa gwamnatin mulkin sojan ƙasar lamba kan ta gudanar da zaɓe tare da maido da mulkin farar hula.

    Bangarorin biyu sun amince da wa'adin mika mulki na watanni 24 a watan Oktoban 2022.

    Majalisar mulkin sojan dai ya rage watanni goma ta shirya zaɓuka da miƙa mulki ga farar hula, kamar yadda jadawalin da Ecowas ya amince da shi.

    • Ƙasashen da aka samu dawowar juyin mulki baya-bayan nan a Afirka
    • Sojoji sun saki fursunonin siyasa a Guinea