Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kamala shirye-shiryen samar da tsaro gabanin yanke hukuncin Kotun Ƙoli kan zaɓen gwamnan jihar da za a yi gobe Juma'a.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa, kwamishinann 'yan sandan jihar CP Usaini Gumel ya ce rundunar ta yi duk abin da ya kamata ta yi domin tabbatar da zaman lafiyar jihar a lokaci da bayan yanke hukuncin.
A ranar Juma' ne kotun ƙolin ƙasar za ta yanke hukunci kan dambarwar zaɓen gwamnan jihar tsakanin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP da Nasiru yusuf Gawuna na APC.
Kwamishinan ya ce rumdumar 'yan sandan jihar ta tattauna da limaman jihar domin tabbatar da yin huɗubar da za ta kwantar da hankulan mutane.
''Kasancewar gobe Juma'ne kuma, kuma a daidai lokacin da ake tafiya sallar juma'a ne ko ake gudanar da sallar ne za a iya yanke wannan hukuncin, mun buƙaci limaman Juma'a da su shirya huɗubobin da su kwantar wa da jama'a hankali'', in ji shi.
CP Usaini Gumel ya ce rundunar 'yan sandan ta kuma tattauna da wakilan jam'iyyun siyasa inda suka tabbatar da cewa za su martaba yarjejeniyar zama lafiyar da suka cimma a kwanakin da suka gabata.
Kwamishinan ya kuma gargadi jama'a da su guji aikata duk wani abu da ka iya tayar da hankulan jama'a a lokaci da bayan yanke hukuncin.
''Ka da ku yarda wani ya tunzuraku don tayar da hankula, domin kuwa duk wanda ya yi hakan za mu yi amfani da kundin tsarin mulki wajen hukunta shi, ba tare da la'akari da jam'iyyarsa ba'', in ji kwashinan.