Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Cutar kwalara ta ɓarke a Zambiya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana samun ƙaruwar fargabar ɓarkewar cutar kwalara a Zambiya bayan da ta bazu zuwa larduna tara daga cikin 10 na kasar.

    Fiye da mutum 300 ne suka mutu, yayin da mutum 8,000 suka harbu da cutar a cikin watannin baya-bayan nan

    ɓarkewar cutar ta baya-bayan nan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar saukar ruwan damina.

    Akwai fiye da marasa lafiya 1,000 a cibiyar kula da marasa lafiya da aka kafa a filin wasan ƙwallon ƙafa da ke Lusaka babban birnin ƙasar.

    Ƙungiyar bayar da agaji ta 'Charity Water Aid'' ta ce akwai buƙatar tallafi don magance tushen matsalar wanda shi ne samar da tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli.

    Shugaban ƙasar Hakainde Hichilema ya soki abin da ya kira ''yawaitar cunkoson gidaje maras tsari a wasu garuruwan ƙasar''

    Ya yi kira ga 'yan ƙasar da ke ƙaura daga yankunan karkara zuwa garuruwan ƙasar, da su dakatar da wannan ɗabi'a kasancewa a yankunan karkara akwai wadataccen ƙasar noma da ruwan sha mai tsafta.

  3. Burundi ta rufe iyakarta da Rwanda

    Ƙasar Burundi ta sanar da rufe iyakarta da makwabciyarta Rwanda sakamakon tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

    Shugaban ƙasar ya zargi Rwanda da goyon bayan 'yan tawayen da suke kai hare-hare, zargin da Kigalin ta musanta zargin.

    A watan da ya gabata 'yan tawayen Tabara suka kashe mutum 20 da suka haɗa da mata da ƙananan yara a kudu maso yammacin Burundi.

    Ministan Harkokin Cikin Gida a Burundi Martin Niteretse ya bayyana shugaba Paul Kagame na Rwanda a matsayin 'mugun maƙwabci' cikin sanarwar da fitar.

    Dangataka ta yi tsami tsakanin ƙasashen bayan jibge sojin Burundi a Gabashin Kongo don su kare hare-haren 'yan tawayen

  4. 'Kada ku yarda wani ya tunzura ku ku tayar da hankali kan shari'ar zaɓen Kano'

    ..

    Asalin hoton, Facebook/ Abdullahi Haruna Kiyawa

    Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kamala shirye-shiryen samar da tsaro gabanin yanke hukuncin Kotun Ƙoli kan zaɓen gwamnan jihar da za a yi gobe Juma'a.

    Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa, kwamishinann 'yan sandan jihar CP Usaini Gumel ya ce rundunar ta yi duk abin da ya kamata ta yi domin tabbatar da zaman lafiyar jihar a lokaci da bayan yanke hukuncin.

    A ranar Juma' ne kotun ƙolin ƙasar za ta yanke hukunci kan dambarwar zaɓen gwamnan jihar tsakanin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP da Nasiru yusuf Gawuna na APC.

    Kwamishinan ya ce rumdumar 'yan sandan jihar ta tattauna da limaman jihar domin tabbatar da yin huɗubar da za ta kwantar da hankulan mutane.

    ''Kasancewar gobe Juma'ne kuma, kuma a daidai lokacin da ake tafiya sallar juma'a ne ko ake gudanar da sallar ne za a iya yanke wannan hukuncin, mun buƙaci limaman Juma'a da su shirya huɗubobin da su kwantar wa da jama'a hankali'', in ji shi.

    CP Usaini Gumel ya ce rundunar 'yan sandan ta kuma tattauna da wakilan jam'iyyun siyasa inda suka tabbatar da cewa za su martaba yarjejeniyar zama lafiyar da suka cimma a kwanakin da suka gabata.

    Kwamishinan ya kuma gargadi jama'a da su guji aikata duk wani abu da ka iya tayar da hankulan jama'a a lokaci da bayan yanke hukuncin.

    ''Ka da ku yarda wani ya tunzuraku don tayar da hankula, domin kuwa duk wanda ya yi hakan za mu yi amfani da kundin tsarin mulki wajen hukunta shi, ba tare da la'akari da jam'iyyarsa ba'', in ji kwashinan.

  5. Jirgin da zai kai tawagar Gambia Afcon ya yi saukar gaggawa

  6. 'Yan sandan Najeriya sun hana amfani da sarar ''No gree for any body''

    .

    Asalin hoton, Nigeria Police Force/Facebook

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta haramta amfani da wata sara da mafi yawan matasan ƙasar ke amfani da ita ta ''No gree for any body'' da ke nufin “kar ka ɗaga wa kowa ƙafa”.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ƙasar, Muyiwa Adejobi, ya ce an ɗauki wannan matakin ne saboda zargin cewa “sarar ta samo asali ne daga mutanen da ke son kawo juyin juya hali a Najeriya.”Tun da aka shiga sabuwar shekara ta 2024 ne dai matasa ke amfani da sarar

    Adejobi, ya ƙara da cewa jami'an tsaro sun ɗauki sarar a matsayin babbar barazana ga tsaro.

  7. Isra'ila ta ci gaba da ruwan boma-bomai a Gaza

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Isra'ila sun ce gaba da hare-haren boma-bomai a kudancin yankin Zirin Gaza, inda aka samu manya-manyan hare-hare ta sama a birnin Khan Younis.

    Ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce fiye da mutum 60 ne aka kashe tun jiya Laraba

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan Falasɗinawa miliyan biyu ne suka rasa muhallansu tun bayan fara yaƙin

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargaɗin cewa ƙaruwar hare-haren boma-boman na ƙara tsananta ayyukan agaji a yankin.

    Haka kuma ana ci gaba da samun musayar makamai masu linzami da rokoki tsakanin dakarun ƙungiyar Hezbollah a Lebonan da sojojin Isra'ila.

  8. Yadda mutane suka wawashe manyan kantuna da ƙona motoci a Papua New Guinea

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

    Aƙalla mutum takwas ne suka mutu bayan wani babban yamutsi ya kaure a Port Moresby babban birinin Papua New Guinea.

    An yi ta cinna wa shaguna da ƙananna motoci wuta, tare da wawashe manyan kantuna, bayan da 'yan sandan ƙasar ke yakin aiki kan albashi.

    Rashin 'yan sandan ya sa mutane a wajen birnin sun yi ta far wa kantunan birnin tare da lalata su kamar yadda mazauna birnin suka shaida wa BBC.

    Rikicin na zuwa ne a yayin da ƙasar ke fama da ƙaruwar tsadar rayuwa da rashin aikin yi tsakanin al'ummar ƙasar.

  9. An ba da umarnin ƙara yawan jami'an tsaro a kan titin Abuja zuwa Kaduna

    .

    Asalin hoton, Yan sandan Najeriya

    Bayanan hoto, ''Yawan jami'an tsaro a kan hanyar zai rage ayyukan 'yan bindiga da ke kai hari a kan hanyar''

    Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ya bayar da umarnin ƙara yawan jami'an tsaro a kan titin Abuja zuwa Kaduna, a wani mataki na tsaurara matakai domin inganta zaman lafiya da tsaro a kan titin.

    Da yake nuna muhimmancin samar da tsaro domin zirga-zirga a yankin, babban sifeton 'yan sandan ya ce za a ƙara girke ƙarin jami'an 'yan sanda da kayan aiki, musamman kayan fasahar zamani da sauran dabarun aiki don inganta tsaro a kan titin.

    Mista Egbetokun ya kuma jaddada cewa ɗaukar wannan matakin zai taimaka wajen tabbatar da tsaron lafiyar 'yan ƙasa da fasijoji.

    Ya ƙara da cewa ganin yawan jami'an tsaron a kan hanyar zai rage ayyukan 'yan bindigar da ke kai hari a kan hanyar.

    Babban sifeton ya yi kiran haɗin kai tsakanin jami'an tsaro da al'ummar garuruwan da ke yankin, yana mai shawartar mutanen su riƙa lura da shige da ficen mutane a garuruwansu, tare da kai rahoton duk wani mutum da ba su yarda da shi ba.

    Ya kuma ce ya kamata jama'ar garuruwan su riƙa haɗa kai da jami'an tsaro domin tabbatar da tsaro da zaman lafiyar yankunansu da na fasinjojin da ke bin hanyar.

    Matakin na zuwa ne kwanaki bayan wasu rahotnni sun ce 'yan bindiga sun tare hanyar a kusa da garin Rijana inda suka sace fasinjoji masu tarin yawa.

  10. Kotun Ƙoli ta tabbatar nasarar gwamna Umo Eno na Akwa Ibom

    .

    Asalin hoton, Pastor Umo Eno/X

    Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da Umo Eno na jam'iyyar PDP a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan jihar Akwa Ibom, bayan ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyu uku suka shigar gabanta suka ƙalubalantar nasararsa a zaɓen ranar 18 ga watan Maris din 2023.

    Kotun Ƙolin ƙarƙahsin jagorancin mai shari'a Uwani Abba-Aji ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyun APC da YPP da lkuma AA, suka shigar a gabanta, suna zargin gwamnan da rashin cancantar tsayawa takara saboda zargin mallakar takardar shaidar karatu ta bogi, zargin da gwamnan ya musanta.

    Tun da farko kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar da suka shigar suna ƙalubalantar zaɓen fitar da gwanin da ya tsayar da Umo Eno a matsayin ɗan takarar PDP.

    Kotun ta kuma yi watsi da ƙarar sannan ta buƙaci a biya wanda ya kai ƙarar naira miliyan 15.

    A ranar Juma'a ne Ƙotun Ƙolin za ta yanke hukunci kan zaɓukan Kano da Zamfara da Plateau da wasu jihohin ƙasar.

  11. An saka dokar ta-ɓaci ta mako biyu a Papua New Guinea bayan ɓarkewar rikici

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Papua New Guinea ya ƙaddamar da dokar ta-ɓaci ta tsawon mako biyu sakamakon rikicin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum shida.

    Firaminista James Marape ya ce sun tanadi dakaru 1000 daga ma'aikatar tsaro, cikin shirin ko-ta-kwana har nan da kwana 14.

    Rikicin ya ɓarke ne a Port Moresby babban birnin ƙasar a ranar Laraba bayan 'yan sanda da sojoji da masu tsaron gidan yari sun gudanar da zanga-zangar dakatar da albashinsu.

    Mista Marape ya bayyana cewar rashin 'yan sanda ne ya haifar da zanga-zangar da wawason dukiya.

    An dakatar da wasu daga cikin manyan jami'an da suke da hannu a rikicin biyan albashin.

  12. Kotu ta bayar da belin tsohon ministan lantarkin Najeriya

    Olu Agunloye

    Asalin hoton, Facebook/Olu Agunloye

    Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye kan kuɗi naira miliyan 50.

    Da yake yanke hukunci a yau Alhamis, mai shari'a Jude Onwuegbuzie na babbar kotun, ya buƙaci tsohon ministan da ya gabatar da mutane biyu waɗanda za su tsaya masa

    An gurfanar da Agunloye ne a gaban kotu ranar Laraba, bisa zargin almundanar kuɗi da ya kai dala biliyan shida a badaƙalar kwangilar wutar Mambila.

    Mai shari'ar ya ce dole ne mutanen su kasance masu hannu da shuni waɗanda kuma ke zaune a Abuja.

    Ya ce tilas ne kuma su mallaki kadarorin da ya kai Naira miliyan 300 tare da takardar shaidar zama wanda za a iya tantancewa.

    "Dole ne kuma su miƙa kwafin katin shaidarsu da kwafin fasfo ɗin su na ƙasashen waje ga kotu," in ji Onwuegbuzie.

    An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 12 ga watan Febrairu.

    • Binciken BBC ya gano ba a fara aikin wutar Mambila ba shekara 40 da fara maganar aikin
    • Dalilan da suka sa Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai Betta Edu
  13. Iran ta sanar da kama jirgin dakon mai a gaɓar ruwan Oman

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Kafar yaɗa labaran Iran ta sanar da cewar ƙasar ce ta kama jirgin dakon man a gabar ruwan Oman a yau Alhamis.

    Rahotannin sun bayyana cewar Kotun Iran ce ta bayar da umarnin kame jirgin.

    An tafka rikicin tsawon shekara ɗaya kan St Nikolas, daga bisani ma'aikatar shari'ar Amurka ta kama ganga miliyan ɗaya ta ɗanyen man Iran.

    Jirgin ya taso ne daga Iraq kan hanyarsa ta zuwa Turkiyya, amma mutanen sun umarce shi ya canza hanya zuwa Iran.

    Cikin makonnin nan jiragen ruwa a ɓangaren tsibirin Larabawa na fuskantar hare-haren ƴan tawayen Houthi da Iran ta ke marawa baya.

  14. Ƙayatattun hotuna daga faɗin duniya na 2023

  15. Ƴan bindiga sun kashe dagaci da ɗansa a Katsina

    Ƴan bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan bindiga sun afkawa kauyen Kukar Babangida da ke karamar hukumar Jibia na jihar Katsina, inda suka kashe dagacin kauyen Magaji Haruna da ɗansa.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kuma kashe wasu mutum takwas a harin da aka kai da misalin karfe 10 na dare ranar Laraba.

    Har ila yau, wani mazaunin garin ya bayyana cewa an tafi da mata wanda ba a san adadinsu ba zuwa yanzu.

    Mazauna garin sun yi imanin cewa akwai manyan shugabannin ƴan bindiga biyu da ke cin karensu babu babbaka a ciki da wajen karamar hukumar ta Jibia.

    Ƙauyen Kukar Babangida ya kasance ɗaya daga cikin kauyuka da ke fama da matsalar ƴan bindiga tun bayyanar ayyukansu a faɗin jihar.

    • 'Yan bindiga sun hana mu girbe amfanin gona'
    • 'Rashin haɗin kan gwamnatoci dama ce ga 'yan bindiga'
  16. Kotun Duniya na sauraron tuhumar da ake yi wa Isra'ila kan kisan ƙare-dangi a Gaza

    Isra'ila

    Asalin hoton, EPA

    Lauyoyin gwamnatin Afirka ta Kudu na gabatar da jawabi a gaban babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya a shari’ar da ake yi wa Isra'ila kan zargin cewa sojojinta sun aikata kisan ƙare-dangi a Gaza.

    Sun faɗa wa Kotun Duniya da ke Hague cewa watanni uku na lugudan wuta da Isra'ila ta ɗauka tana yi a Gaza, ya saba wa yarjejeniyar hana kisan kare dangi ta 1948.

    Sun kuma yi zargin cewa Isra'ila na da niyyar aikata kisan kare dangi a kan Falasɗinawa a Gaza, wanda ta rena a matakin koli na ƙasa. Sai dai Isra'ila ta yi watsi da batun inda ta ce ba shi da tushe.

    A ranar Juma'a ne lauyoyinta za su fara mayar da martani. Afirka ta Kudu dai na kira da a dakatar da kai farmakin sojin Isra'ila cikin gaggawa.

  17. China ta gargaɗi Taiwan kan zaɓar ɗan takarar da zai gurgunta alaƙar ƙasashen

    China ta fitar da kakkausar sanarwa kan Taiwan, kwanaki biyu gabannin zaɓen shugaban ƙasa a can, inda ta ce idan wanda ke sahun gaba ya yi nasara hakan babbar barazana ce ga alaka tsakaninta da Beijing.

    Ofishin harkokin China a Taiwan ya ce yana fatan yawancin 'yan Taiwan za su gane abin da ta jima ta na nunawa, cewa kar su zaɓi jam'iyyar Democratic Progress, wadda ɗan takararta William Lai ko Lai Ching-te ya kasance babban mai sukar gwamnatin China.

    Shi kuwa babban ɗan adawa Hou Yu-ih, ya sha gargaɗin ƴan ƙasar kar su zaɓi Mr Lai, wanda babbar barazana ce ga alakarsu da China da ke kallon Taiwan a matsayin wani bangare na kasarta.

  18. Kotu a Najeriya ta yanke wa ɗan kirifto ɗaurin shekara biyar a gidan yari

    ...

    Asalin hoton, X/EFCC

    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa ɗan kirifto mai suna Benjamin Ikaa ɗaurin shekara biyar a gidan yari.

    Mai shari'a Emeka Nwite na kotun ne ya yanke masa hukuncin bayan samunsa da laifin damfarar $1.6m.

    Benjamin Ikaa ya amsa laifin ɗaya daga cikin laifukan da aka tuhumesa da shi.

    Sai dai yana da zaɓin biyan tarar naira miliyan biyar.

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta fara kama Ikaa a shekarar da ta gabata kan zargin tafiyar da wani shafin yanar gizo na kirifto, inda yake yi wa mutane alkawarin ninƙa musu kuɗaɗe idan suka zuba jari, abin da ya janyo suka rasa makudan kuɗaɗe.

    Benjamin ya miƙa mota ƙirar Toyota Avalon da kuma wayar iPhone 13 ga gwamnatin tarayya.

    An kuma gano $11,000 a hannunsa inda za a mayar wa mutanen da ya damfara kuɗin.

    Waɗanda ya damfara sun fito ne daga Afrika ta Kudu, Norway, Birtaniya da kuma tsibirin Barbados.

    • 'Gagarumin ɗan kirifto ya koma cin burodi da ruwa'
    • Kotu ta ɗaure matashi ɗan kirifto a Kaduna saboda zamba ta Instagram.
  19. An kama sojojin da suka azabtar da farar hula a jihar Ribas

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar sojin Najeriya ta kama wasu jami'anta biyu bayan da wani bidiyo ya nuna suna azabtar da farar hula a jihar Ribas.

    Bidiyon wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna wani sanye da kakin soji da kuma wani cikin kayan farar hula suna azabtar da wani mutum, duk da hakuri da ya yi ta ba su.

    Mutumin ya yi ta kuka yana faɗin cewa: "A'a, don Allah ku yi hakuri, zan faɗi gaskiya."

    Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ranar Laraba, ta nuna ɓacin ranta kan abin da jami'an biyu suka aikata inda ta ce ba za ta lamunci irin haka ba.

    "Muna so mu tabbatar da cewa mun kama sojojin da suka aikata wannan abu na saɓa ka'idar aiki," in ji sanarwar.

    Mutane da dama sun yi Alla-wadai da abin da jami'an sojin suka aikata bayan da bidiyon ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda wani mai amfani da shafin X ya kwatanta ɗabi'un sojojin da "Rashin imani da kuma saɓa ka'idar aiki".

    Sojojin sun tabbatar da cewa za su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da yin alkawarin hukunta waɗanda suka aikata laifin.

    A baya, ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam na ƙasa da ƙasa sun sha sukar sojojin Najeriya kan zargin take ƴancin ɗan'adam da ya haɗa da azabtarwa, tsarewa da kuma kashe-kashe ba bisa ƙa'ida ba.

    • Aikinmu kare mutane ne ba kashe 'yan ƙasa ba - Babban hafsan tsaron Najeriya
    • 'Muna bincike kan zargin rashin bai wa sojojinmu isasshen abinci'
  20. Trump ya sake ƙin halartar muhawarar ƴan takarar Republican

    Zaɓen Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    An gudanar da muhawarar 'yan takarar shugaban ƙasa karkashin jam'iyyar Republican da za su kalubalanci Joe Biden a zaen watan Nuwamba mai zuwa, sai dai Donald Trump ya tankwaɓar da goron gayyatar shiga.

    Gwamnan jihar Florida Ron DeSantis da tsohuwar jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley sun yi musayar kalamai kan batutuwa da dama, amma sun yi gum da bakinsu kan sukar Mr Trump wanda ya mamaye zaɓen.

    Ms Haley ta ce a bayyane ya ke Trump ya sha kaye a zaɓen 2020, kuma za ta mayar da Amurka kan turba madaidaiciya.

    Mr DeSantis na da ra'ayin cewa zaɓar Donald Trump zai janyo a yi ta tattauna batun halayen da ya nuna na baya da batun shari'ar da ake yi ma sa.