Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce kimanin mutum 10,000 ne aka bayar da rahoton mutuwarsu cikin watan Disamban da ya gabata sakamakon cutar korona.
WHO ta ce har yanzu annobar covid na zama wata babbar barazana duk kuwa da wucewarta.
Hukumar ta ce alƙaluma daga wasu majiyoyi sun nuna cewa an samu ƙaruwar yaɗuwar cutar a cikin watan da ya gabata, sakamakon tarukan bukukuwan kirsimeti, inda aka samu ƙarin yaɗuwar cutar nau'in JN.1, wanda a yanzu ya fi kowane nau'in cutar bazuwa a duniya.
Shugaban hukumar Lafiyar ta Duniya Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ''duk da cewa a yanzu cutar ba ta yi wa duniya barazana, amma har yanzu cutar na ci gaba da yaɗuwa tare da kashe mutane a duniya''.
Baya ga rahoton kashe kusan mutum 10,000 cikin watan daga ya gabata, an samu ƙarin kashi 42 na mutanen da aka kwantar a asibiti, yayin da aka samu ƙarin kashi 62 na waɗanda aka kwantar a ɗakunan masu buƙatar kulawa ta musamman idan aka kwatanta da watan Nuwamban shekarar da ta gabatan.
Dakta Dedros ya ce wani abin tayar da hankali shi ne an tattaro waɗannan alƙaluma ne daga ƙasashe biyar kawai waɗanda mafi yawancinsu daga nahiyar Turai da Amurka.
"Hakan na nufin akwai yiwuwar cewa an samu ƙari a wasu ƙasashen da ba mu samu rahotonsu ba'', in ji Tedros.
Ya ƙara da cewa ya kamata a ɗauki matakan kariya daga sauran cutuka a gwamnatance da ɗaiɗaiku, ya zama wajibi mu ci gaba da ɗaukar matakai kan cutar corona.
"Duk da cewa mutuwar mutum 10,000 a wata guda, bai kai adadin mutanen da suke mutuwa ba a lokacin ganiyar annobar, dole a ɗauki mataki don magance wannan matsalar'', in ji shi.
Dakta Tedros ya buƙaci gwamnatoci su ci gaba da lura da gwaji da riga-kafin cutar da ake yi musu a ƙasashensu, don tabbatar da cewa yana isa ga mutane.
"Ya kamata mu ci gaba da kira ga mutane da su je domin karɓar allurar riga-kafi tare da yi musu gwaji , su kuma ci gaba da sanya takunkumai da tabbatar da cewa ba a riƙa shiga cikin cunkoson jama'a ba'', in ji shi.
A watan Mayun 2023 ne dai WHO ta ayyana kawo ƙarshen annobar corona a duniya, fiye da shekara uku da ɓullar cutar karon farko a birnin Wuhan na ƙasar China a ƙarshen shekarar 2019.