Ministar jin ƙai ta Najeriya, Betta Edu, wadda Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya dakatar ta bayyana a ofishin hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) domin amsa gayyata.
Bayan dakatar da ita ne Shugaba Tinubu ya bai wa shugaban EFCC, Ola Olukayede umarnin yin bincike kan duk hada-hadar kuɗin da ma'aikatarta ta yi da dukkan hukumomin da ke ƙarƙashinta.
An dakatar da ita ne wata shida da hawan ta kan muƙamin saboda zarge-zargen karkatar da kuɗaɗe da aka ware domin amfanin al'umma.
Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa a cikin wata takarda ce ministar ta bayar da umarnin tura maƙudan kuɗi zuwa asusun ajiyar banki na wani kamfani mai zaman kansa, kuɗin da suka kai fiye da naira miliyan 585.
Tun lokacin ne kuma al'ummar Najeriya suke ta ce-ce-ku-ce kan lamarin.
Betta Edu, mai shekara 36 ta kasance minista ta farko a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu da ta fuskanci irin wannan suka daga jama'a saboda zarge-zargen da ake tuhumar ta da aikatawa.
Matakin dakatarwar ya zo ne ƙasa da mako ɗaya da dakatar da shugabar hukumar bayar da tallafin dogaro da kai ta Najeriya, wato National Social Investment Programme Agency, Halima Shehu, wadda ita ma aka yi zargin da hannunta a badaƙalar halasta kuɗin haram.
Betta Edu wadda ƴar asalin jihar Cross River ne a kudu maso kudancin Najeriya, an haife ta ne a ranar 27 ga watan Oktoban 1986.
An haife ta ne a London sai dai a lokacin da take shekara takwas, ta koma Najeriya tare da ƴan'uwanta da iyayenta.
Su biyar ne a wajen iyayenta kuma tana da abokin tagwaitaka.
Ƙwararriya ce a fannin tsarawa da tafiyar da harkar lafiya kuma tana da gogewa ta fiye da shekara 12 kan jagoranci.
Betta ta kammala karatun Firamare a makarantar Charles Walker a shekarar 1995.
A 2001 ne ta kammala sakandare a makarantar mata ta gwamnatin tarayya da ke birnin Calabar.
Daga nan kuma ta soma karatun jami'a inda ta gama karatun digiri a fannin likitanci daga jami'ar Calabar da ke jihar Cross River.
Dr Betta ta yi karatu bayan kammala digirinta inda a shekarar 2014 ta samu babbar difloma kan fannin lafiyar al'umma a ƙasashe masu tasowa daga kwalejin koyon aikin tsafta a London da ke Birtaniya
A dai shekarar ce kuma ta yi digiri na biyu a ɓangaren lafiyar al'umma daga kwalejin koyon aikin tsafta da ke London.
Sannan ta yi digiri na uku a fannin lafiyar al'ummar daga jami'ar Texila American University.
Tana bijiro da tsare-tsare masu tasiri kan fannin lafiya a matakin jiha da kuma ƙasa.
A lokacin da ta yi aiki ƙarƙashin gwamnatin Cross River daga 2015 zuwa 2016, ita ce mai bai wa tsohon gwamnan jihar Ben Ayade shawara mafi ƙarancin shekaru.
Tsohon gwamnan ya kuma naɗa ta a matsayin kwamishinar lafiya daga 2019 zuwa 2022 kafin ta ajiye aiki domin tsunduma harkokin siyasa gadan-gadan.
- Dalilan da suka sa Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai Betta Edu