Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Mukhtar Adamu Bawa and Usman Minjibir

  1. Tuhumar aikata kisan ƙare dangi ' ba ta da tushe' - Blinken

    Sakataren Wajen Amurka Antony Blinken ya ce "tuhumar aikata kisan ƙare dangi da ke gaban kotun duniya ba shi da tushe balle makama."

    Waɗanda ke far wa Isra'ila, kamar Hamas da Houthi, a cewarsa, "a fili suna ci gaba da kiran a shafe ƙasar Isra'ila kuma a kashe ɗumbin Yahudawa".

    Ya ce faɗan da ake yi musamman yana wahala a Gaza "saboda Hamas tana ɓoyewa tare da harba makamai daga makarantu da asibitoci".

  2. ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jakadan Saudiyya a Birtaniya, Yarima Khalid bin Bandar Al-Saud ya ce babu wata maslaha da ta fi dacewa game da yadda Gaza za ta kasance bayan yaƙi.

    Yarima Khalid ya bayyana haka ne a lokacin da yake yi wa BBC Radio 4 jawabi.

    Da aka tambaye shi kan rawar da Saudiyya - wadda ta kusa daidaita alaƙar diflomasiyyarta da Isra'ila kafin 7 ga watan Oktoba - za ta taka a yankunan Falasɗinawa a gaba, ya ce ba zai yiwu a iya tsara hakan ba ba tare da an dakatar da yaƙi ba.

    Ya ce "Yadda za a tsara hakan, ta ina hakan zai samu, wannan dole ne a tattauna da Falasɗinawa da kasashen duniya kuma ba tantama hakan ba za ta faru ba sai Isra'ila ta amince da shi."

    Da aka tambaye shi ko yana ganin Hamas na iya shiga harkar tafiyar da ƙasar Falasɗinu idan ta samu, ya nuna cewa za su iya shiga a wasu lokutan.

  3. Zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar kafa ƙasar Falasɗinawa, cewar Blinken

    Anthony Blinken ya ci gaba da bayyana yayin jawabi a wani taron manema labarai da ya gabatar lokacin da yake ziyara a Isra'ila, ganawar da ya yi a yau Talata, inda ya ce ya zanta da Benjamin Netanyahu game da zaman ɗar-ɗar da Lebanon.

    Ya ce ya faɗa wa majalisar ministocin yaƙi ta Isra'ila cewa Amurka tana goyon bayan ƙasarsu a ƙoƙarinta na tabbatar da tsaro a kan iyakarta ta arewaci kuma ta ƙuduri aniyar aiki Isra'ila don gano masalahar diflomasiyya da nufin samun tsaro a Isra'ila da Lebanon.

    Zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar wata hanya da za ta kai ga kafa ƙasar Falasɗinawa, in ji shi, kuma hakan na buƙatar tunkarar lamarin da haɗin gwiwar ɗaukacin yanki.

    A cewarsa, ana iya cimma wannan buri amma idan an haɗa kai wajen bin kadin lamarin.

    "Jazaman ne Isra'ila ta kasance abokiyar ƙawance ga shugabannin Falasɗinawa, waɗanda ke shirye su jagoranci al'ummarsu don zama kafaɗa da kafaɗa cikin zaman lafiya da Isra'ila a matsayin maƙwabta," in ji Blinken.

  4. Za a gurfanar da ɗan ƙungiyar asiri a Kenya

    Wata kotu a Kenya ta bai wa mai gabatar da ƙara wa'adin makonni biyu ya gurfanar da shugaban ƙungiyar asiri da ke ɗaure a gidan yari ko kuma a bayar da belinsa.

    An tsare Paul Nthenge Mackenzie tun a watan Afrilun da ya gabata sakamakon mutuwar akalla mutane 400, waɗanda da dama daga cikinsu suka kashe kansu da yunwa.

    Binciken da jami'ai suka gudanar ya gano alamun shaƙewa da duka a jikin wasu gawarwakin.

    Wadanda suka rasa rayukan nasu mabiya ne a Cocin Good News International da ke gabar tekun Kenya.

    Mista Mackenzie dai ya musanta aikata laifi.

  5. David Cameron ya yi kira ga Isra'ila ta mayar wa Gaza ruwan sha

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakatare harkokin wajen Burtaniya, kuma tsohon firaiministan ƙasar, David Cameron ya ƙi amincewa da ganin wata shawara da ofishin cikin gidan Burtaniya ya fitar da ke cewa Isra'ila ta karya dokokin ƙasa da ƙasa, a fannin jinƙai a Gaza.

    Da yake magana kan 'yan majalisar dokoki, Sakataren Harkokin wajen ya ce ba haƙƙinsa ba ne "yin fashin baƙin dokoki".

    Mista Cameron ya ƙara da cewa ya ga abubuwa lokacin yaƙin da ke da "taɓa zuciya" sannan ya yi kira ga Isra'ila da ta mayar wa da Gaza ruwan sha.

    To sai dai ya ce ba zai yarda a sanya shi tattauna ko Isra'ila ta karya dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, yana mai cewa " kawai dai wani abu ne da ya kamata a ce sun yi, a ra'ayina."

  6. Jagoran adawar Najeriya ya yaba wa Tinubu

    Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da ya wuce na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya ce matakin dakatar da ministar jin ƙai da yaƙi da talauci, Betta Edu, abin yabawa ne,ko da yake bai isa ba.

    Shugaba Tinubu ya dakatar da ministar ne a jiya Litinin kuma ya umarci hukumar EFCC ta gudanar da bincike a kanta, bayan ya fuskanci kiraye-kirayen a ɗauki mataki a kanta saboda zarge-zargen tafka almundahana, ko da yake ta musanta zarge-zargen.

    Ministar da aka dakatar ta dai fuskanci gagarumar suka ne bayan kwarmata wasu takardun kashe kuɗi daga ma'aikatarta, waɗanda suka nuna ta bayar da umarni ga babbar akanta ta biya naira miliyan 585 cikin wani asusun ajiyar wata, lamarin da ake zargin ya saɓa ƙa'idojin kashe kuɗi na gwamnati.

    A cikin wata wasiƙa da wani mataimakinsa na musamman Phrank Shaibu ya fitar, jagoran adawar Najeriya ya ce abin takaici ne ganin yadda shirin da aka kafa don tsamo 'yan Najeriya miliyan 100 daga matsanancin talauci amma kamar yadda ake zargi ya zama saniyar tatsa ga gwamnatocin jam'iyyar APC.

    Ya ce, “Ko da yake Tinubu ya cancanci yabo saboda dakatar da Betta Edu, amma mun yi imani, yunƙurin ya zo a makare. Da farko, ba shi da wata alaƙa ta naɗa ta a matsayin minista ta irin wannan muhimmiyar ma'aikata. Sai dai Tinubu ya fifita siyasa a kan ƙwarewa, lamarin da ya janyo wannan abin kunya.

    Atiku wanda ya yi kira a yi wa ma'aikatar garambawul, ya kuma yi zargin cewa ba Betta Edu kaɗai ba ce da hannu a wannan badaƙala.

  7. Boniface ba zai buga wa Super Eagles Afcon ba

  8. Shugaban Hamas ya nemi taimakon makamai daga ƙasashen Musulmi

    Haniyeh

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban ƙungiyar mayaƙan Hamas, "Isra'ila ta gaza cimma burinta" a yaƙin da take yi da Gaza.

    Ismail Haniyeh ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na shugabannin Musulmi a ƙasar Qatar, inda yake zaune.

    Haniyeh ya musanta cewa harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba ya faru ne "sakamakon wani yunƙurin nuna wa Falasdinawa wariya".

    Dangane kuma da 'yan Isra'ilar da ake garkuwa da su, Isma'il Haniyeh ya ce Isra'ila " ba za ta taɓa gano mutanen ba har sai sun saki dukkan fursunoninmu da ke hannunsu".

    A wani jawabin kuma na daban da ƙungiyar ta Hamas ta saki, Haniyeh ya yi kira ga ƙasashen Musulmi "da su taimaka wa Hamas da makamai, saboda wannan......ba yaƙin al'ummar Falasɗinawa ba ne su kaɗai".

    • Wane ne jagoran Hamas da aka kashe a Beirut?
    • Wane ne Yahya Sinwar shugaban Hamas na Gaza?
  9. Najeriya ta lalata hauren giwa na ƙimar dala miliyan 11

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta lalata tarin hauren giwa mai ƙimar tsabar kuɗi har dala miliyan 11 da ta ƙwace daya hannun masu fasa-ƙwauri.

    An dai yi fasaƙwaurin hauren ne daga ƙasashen Afirka masu dama.

    Ministan Muhalli na Najeriyar, Iziaq Adekunle Salako wanda ya shaida hakan yayin wani taro a Abuja, ya ce ya ɗauki matakin lalata tarun hauren giwar ne domin aikewa da saƙo da ke nuna rashin amincewarsu ga irin wannan aiki.

    Ko a watan Oktoba ma sai da aka lalata tan-tan na ɗan kunya da aka ƙwace daga hannun masu simoga.

    Masana sun ce ana kashe dubban ɗaruruwan giwaye a kowace shekara domin yin safarar haurensu, duk da haramcin cinikayyarsu da duniya ta yi shekaru da suka gabata.

    Masu kare dabbobi sun ce Najeriya ta zamo a gaba-gaba wajen safarar sassan dabbobi.

  10. Za a ɗaure da yi wa matashin da ya yi waƙar cire hijabi bulala a Iran

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An yanke wa wani mawaƙi, Mehdi Yarrah ɗan ƙasar Iran hukuncin ɗaurin fiye da shekaru biyu a gidan yari tare da bulala 74, bisa laifin sakin wata waƙa mai ƙwararawa mata gwiwa su cire hijabinsu.

    Lauyan Mehdi Yarrahi ya ce an tuhumi mawaƙin ne da laifin rarraba wata waƙa ba bisa ƙa'ida ba wadda take kakkausar suka ga hallaya da al'adun ƙwarai na ƙasar Iran.

    An dai saki waƙar mai taken 'Your Headscarf' wadda ke nufin hijabinku a kusan lokacin tunawa da rasuwar Mahsa Amini.

    Mahsa dai ta rasu ne bayan da aka tsare ta bisa zargin karya dokar ƙasar Iran ta sanya hijabi.

    Mutuwar Mahsa dai a watan Satumban 2022 ta janyo zanga-zanga da tarzoma ta 'yan watanni.

    • Ranar Hijabi ta Duniya: 'Abin da hijabi ke nufi a wurinmu'
    • 'Ana tsangwama ta saboda ni ƴar rawa ce kuma mai sa Hijabi'
  11. Tinubu ya rage yawan masu rakiya a tafiye-tafiyensa

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da sanarwar rage yawan jami'an da za su riƙa yi masa rakiya a duk tafiye-tafiyen aiki da zai je ciki da wajen ƙasar.

    Matakin ya shafi dukkan ministoci da manyan jami'an gwamnatinsa ciki har da mataimakin shugaban ƙasa da uwargidan shugaban ƙasa.

    Sanarwar wadda Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaban Najeriya kan harkar yaɗa labarai ya fitar ranar Talata na cewa matakin, wani yunƙuri ne na rage yawan kuɗaɗen da jami'an gwamnati ke kashewa kan harkokin tafiye-tafiye.

    Ta ce yawan jami'an da za su riƙa yi wa shugaban ƙasa rakiya zuwa ƙasashen waje, nan gaba ba za su wuce jami'ai 20 ba. Haka zalika, Ngelale ya ce Tinubu ya ba da umarnin a daina tura ɗumbin jami'an tsaro zuwa wata jiha a duk lokacin da zai kai ziyara can, maimakon haka za a riƙa amfani da jami'an tsaron da ke jihar ne kawai don tabbatar da tsaro.

    • Sayen motocin alfarma na Remi Tinubu na tayar da ƙura a Najeriya
    • Me Tinubu zai yi da bashin kusan dala biliyan takwas da zai karbo?
  12. Muna son a rage kashewa da jikkata fararen hula a Gaza - Blinken

    ..

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya ce akwai batutuwa da dama da yake so a duba yayin taro a birnin Tel Aviv, a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza.

    Mista Blinken yayin wata ganawa da shugaban Isra'ila, Isaac Herzog, ya jaddada muhimmancin rage hare-haren da suke jikkata fararen hula a Gaza.

    Ya ƙara neman Isra'ilar ta samar da kafar shigar da kayan agaji.

    Wasu manyan wakilan ƙasashen Turai dai sun ce, ƙulla yarjejeniya a tsakanin yankuna gabaɗaya, ita ce hanyar samar da mafita a rikicin.

    Mista Blinken zai gana da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da mukarraban gwamnatinsa, kafin ganawarsa da iyalan wasu daga cikin 'yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su a Gaza, dangane da hanyoyin da za a bi wajen ganin an sako su.

  13. "Shekarar 2023 ce wadda ta fi ɗumamar yanayi"

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Kula da Sauyin Yanayi ta Kungiyar Tarayyar Turai, Copernicus ta tabbatar da shekara ta 2023 a matsayin shekarar da ta fi kowacce ɗumamar yanayi .

    Kusan rabin shekarar da ta gabata, an fuskanci yanayi da ƙarin sama da ɗigo ɗaya a ma'aunin Celsius fiye da yadda aka saba kafin juyin-juya-halin-masana'antu.

    BBC ta gano cewa watannin farko na shekara ta 2023 sun yi bazata a sauyin yanayin da duniya ke fuskanta, abin ya sauya a watan Yuli lokacin da duniya ta fara fuskantar ɗumamar yanayi.

    Babban ƙudurin Yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris ita ce taƙaita ɗumamar yanayi ƙasa da yadda yake.

    Ofishin Kula da Yanayi na Burtaniya ya ce akwai yiwuwar yanayin zafi a bana zai ninka saboda yanayin El Nino mai rike zafi cikin iska.

    • Dalilin da ya sa zafi ya tsananta a wannan bazarar
    • An yi rana mafi tsananin zafi a tsawon shekara 60 a China
  14. Ana zargin ƴan kasuwa da tsawwala farashin abinci a Gaza

    ...

    Asalin hoton, ANADOLU

    Falasɗinawa na kokawa kan halin da suke shiga a hannun ƴan kasuwa waɗanda ake zargi da tsawwala farashin abinci, yayin da ake matuƙar ƙarancinsa a yankin Gaza.

    Wani mazaunin Gaza mai suna Jihad Abu Sharkh ya bayyana wa BBC cewar ya tsere daga garinsu da ke arewacin Gaza zuwa Rafah da ke kudanci, inda mutane da dama ke neman mafaka - sai dai ya ce abinci a yankin ya gagari talaka.

    "Muna ɗanɗana kuɗarmu a hannun masu sayar da abinci waɗanda ke sayen abinci a kan kuɗi shekel 10 amma su sayar mana kan shekel 300." In ji shi.

    "Misali, sukan sayi buhun fulawa daga masu ajiye ta a kan kuɗi shekel 60, sai su sayar mana a kan shekel 300."

    Ya yi kira ga ƙasashen duniya da su "yaƙi masu sayar da abincin waɗanda suke tsawwala wa al'umma."

    Shi ma Jamal Abu Alyan, wanda ke rayuwa a kudancin Gaza ya ce "duk inda muka je muna fuskantar uƙubar masu sayar da abinci."

    Wani mutum mazaunin Rafah ya shaida wa BBC cewa: "Mutane da dama na kwana ba tare da cin abinci ko ruwan sha ba, yayin da wasu suka zama mabarata na ƙarfi da yaji sanadiyyar ƙarancin abinci da kuma tsawwalawa daga masu sayar da abincin."

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa Gaza na fuskantar matsanancin ƙarancin abinci.

    • Yadda Babban Bankin Ghana ya yi asarar dala biliyan 5 a shekara ɗaya
    • Dalilin da ya sa albasa ta fi nama tsada a Philippines
  15. Donald Trump zai ƙara gurfana a kotu yau

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump zai gurfana a wata kotu da ke birnin Washington domin sanin matsayinsa kan ko yana da kariya daga fuskantar shari'a kan manyan laifuka ko kuma a'a.

    Ana sa ran lauyoyinsa za su shaida wa kotu cewa matsayinsa na wanda ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙasar ya ba shi kariya daga fuskantar shari'a.

    Hukuncin da kotu za ta yanke kan wannan shari'a zai shafi sauran shari'o'i da ake yi wa Mista Trump.

    Masu gabatar da ƙara na ganin cewa jinkiri wajen yanke hukuncin zai haifar da tafiyar hawainiya wajen yanke hukunci kan shari'o'in da ake yi wa Trump a kotu har zuwa bayan zaɓen shugaban ƙasa na watan Nuwamba.

    Ana sa ran sai nan gaba ne kotu za ta sanar da hukuncin da ta yanke kan ƙarar.

    • Kotu ta haramta wa Trump tsayawa takara
    • Trump ya zama shugaban Amurka na farko da aka ɗauki hotonsa a gidan yari
  16. Wace ce Betta Edu, ministar da Tinubu ya dakatar?

    ..

    Asalin hoton, BETTA EDU X

    Ministar jin ƙai ta Najeriya, Betta Edu, wadda Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya dakatar ta bayyana a ofishin hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) domin amsa gayyata.

    Bayan dakatar da ita ne Shugaba Tinubu ya bai wa shugaban EFCC, Ola Olukayede umarnin yin bincike kan duk hada-hadar kuɗin da ma'aikatarta ta yi da dukkan hukumomin da ke ƙarƙashinta.

    An dakatar da ita ne wata shida da hawan ta kan muƙamin saboda zarge-zargen karkatar da kuɗaɗe da aka ware domin amfanin al'umma.

    Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa a cikin wata takarda ce ministar ta bayar da umarnin tura maƙudan kuɗi zuwa asusun ajiyar banki na wani kamfani mai zaman kansa, kuɗin da suka kai fiye da naira miliyan 585.

    Tun lokacin ne kuma al'ummar Najeriya suke ta ce-ce-ku-ce kan lamarin.

    Betta Edu, mai shekara 36 ta kasance minista ta farko a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu da ta fuskanci irin wannan suka daga jama'a saboda zarge-zargen da ake tuhumar ta da aikatawa.

    Matakin dakatarwar ya zo ne ƙasa da mako ɗaya da dakatar da shugabar hukumar bayar da tallafin dogaro da kai ta Najeriya, wato National Social Investment Programme Agency, Halima Shehu, wadda ita ma aka yi zargin da hannunta a badaƙalar halasta kuɗin haram.

    Tarihin Betta Edu

    Betta Edu wadda ƴar asalin jihar Cross River ne a kudu maso kudancin Najeriya, an haife ta ne a ranar 27 ga watan Oktoban 1986.

    An haife ta ne a London sai dai a lokacin da take shekara takwas, ta koma Najeriya tare da ƴan'uwanta da iyayenta.

    Su biyar ne a wajen iyayenta kuma tana da abokin tagwaitaka.

    Ƙwararriya ce a fannin tsarawa da tafiyar da harkar lafiya kuma tana da gogewa ta fiye da shekara 12 kan jagoranci.

    Betta ta kammala karatun Firamare a makarantar Charles Walker a shekarar 1995.

    A 2001 ne ta kammala sakandare a makarantar mata ta gwamnatin tarayya da ke birnin Calabar.

    Daga nan kuma ta soma karatun jami'a inda ta gama karatun digiri a fannin likitanci daga jami'ar Calabar da ke jihar Cross River.

    Dr Betta ta yi karatu bayan kammala digirinta inda a shekarar 2014 ta samu babbar difloma kan fannin lafiyar al'umma a ƙasashe masu tasowa daga kwalejin koyon aikin tsafta a London da ke Birtaniya

    A dai shekarar ce kuma ta yi digiri na biyu a ɓangaren lafiyar al'umma daga kwalejin koyon aikin tsafta da ke London.

    Sannan ta yi digiri na uku a fannin lafiyar al'ummar daga jami'ar Texila American University.

    Tana bijiro da tsare-tsare masu tasiri kan fannin lafiya a matakin jiha da kuma ƙasa.

    A lokacin da ta yi aiki ƙarƙashin gwamnatin Cross River daga 2015 zuwa 2016, ita ce mai bai wa tsohon gwamnan jihar Ben Ayade shawara mafi ƙarancin shekaru.

    Tsohon gwamnan ya kuma naɗa ta a matsayin kwamishinar lafiya daga 2019 zuwa 2022 kafin ta ajiye aiki domin tsunduma harkokin siyasa gadan-gadan.

    • Dalilan da suka sa Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai Betta Edu
  17. EFCC na yi wa Betta Edu tambayoyi kan badaƙalar fiye da N585m

    Ministar jin ƙai, Betta Edu da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar ta bayyana a ofishin hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa kan zargin ta da halalta kuɗin haram.

    Jim kaɗan bayan da shugaba Tinubu ya dakatar da ita ne, hukumar ta EFCC ta yi sammacin ministar ta bayyana a hedikwatar ofishin da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

    Kafafen yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito EFCC ta soma yi wa Edu tambayoyi kan zargin karkatar da naira miliyan 585.

    A cewar bayanan, Edu ta halarci ofishin EFCC tare da mataimakanta da lauyanta.

    Ta bayyana a hukumar ne kwana ɗaya bayan da shugaba Bola Tinubu ya dakatar da ita.

  18. Ƴan siyasa mata da ake zargi da cin hanci da rashawa a Najeriya

  19. Yadda rayuwa take a Gaza cikin hotuna

    ..

    Asalin hoton, Ashraf Amra/Anadolu via Getty Images

    Bayanan hoto, Baƙin hayaki da wuta na tashi daga sansanin ƴan gudun hijra na Al-Maghazi da ke tsakiyar Gaza
    ..

    Asalin hoton, Palestinian Red Crescent Society/Reuters

    Bayanan hoto, Tawagar jami'an ba da agaji daga kungiyar Red Crescent Society ta Falasɗinu yayin da take ƙoƙarin saka wani mutum da ya ji rauni a mota zuwa asibitin al-Aqsa
    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wata mata ke takawa ta gefen ɓuraguzn ani gida da harin Isra'ila ya shafa a Rafah kusa da iyakar Gaza da Masar
    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Yara sun kafa layi domin ɗiban ruwa a Rafah
  20. An tuhumi sojoji kusan 30 kan yunƙurin kifar da gwamnati a Saliyo

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Wata kotu a Saliyo ta tuhumi sojoji 27 da aikata laifuka kan zargin yunƙurin kifar da gwamnati.

    "Tuhume-tuhumen sun haɗa da yin bore da hana yin boren da taimaka wa maƙiya da wasu laifuka," kamar yadda ma'aikatar tsaro ta fada cikin wata sanarwa.

    A watan Nuwamban bara, ƴan bindiga suka far wa wani sansanin sojoji da wasu gidajen yari a Freetown, inda suka saki kusan fursunoni 2,000.

    Hukumomi sun bayyana hakan a matsayin yunƙurin kifar da gwamnati.

    A makon da ya gabata ne aka tuhumi tsohon shugaban ƙasar Ernest Bai Koroma da cin amanar ƙasa.

    Ya musanta hannu a tuhume-tuhumen da suka kai ga kashe mutum kusan 20.

    Hukumomi suna kuma tuhumar ɗaya daga cikin dogarin tsohon shugaban ƙasar tare da tsoffin ƴan sanda 11 da ma'aikatan gidan yari.

    An yi zama kafin soma shari'ar sojojin 27 a wata kotu da ke birnin Freetown. An kuma ɗage zaman zuwa gobe Laraba.

    Tashin hankalin da aka yi a watan Nuwamba ya zo ne watanni biyar bayan zaɓen da Shugaba Julius Maada Bio ya sake lashewa karo na biyu.

    Sai dai ƴan hamayya sun yi watsi da sakamakon zaɓen inda masu sa ido kan zaɓen daga ƙasashen duniya suka soki zaɓen saboda rashin tabbatar da gaskiya.