Zirin Gaza na daf da faɗawa cikin wata sabuwar matsalar ayyukan jin ƙan ɗan'adam idan aka hana kayan buƙatun rayuwa shiga yanki, a cewar hukumomi, yayin da Isra'ila ta mayar da martani ga hare-haren ƙungiyar Hamas.
Mazauna Zirin Gaza sun ce ba a shigar da kayan agaji ba tun ranar Asabar, kuma a ranar Litinin Isra'ila ta ayyana "datse komai gaba ɗaya" a yankin - inda ta ce za a yanke hasken lantarki da shigar da abinci da man fetur da kuma ruwan sha.
Gaza, yanki ne da mutane kimanin miliyan 2.3 ke rayuwa, kuma kashi 80 cikin 100 na mutanen sun dogara ne a kan kayan agaji.
Mutane sama da 500 ne suka mutu a can, yayin hare-haren ramuwar gayya na Isra'ila.
Isra'ila ce ke iko da sararin samaniyar Gaza da gaɓar ruwanta, kuma tana iyakance mutane da kayayyakin da za su iya tsallakawa cikin yankin..
Masar ita ma, tana matukar taƙaita mene ne da kuma wane ne zai tsallaka cikin Gaza, ta hanyar kan iyakarta da yankin.
Tun bayan hare-haren safiyar Asabar, Isra'ila ta dakatar da duk kayan masarufin da ke shiga Zirin Gaza, ciki har da abinci da magunguna. Mutane da dama a yanzu ba su da lantarki da intanet, kuma nan gaba kaɗan ba za su iya samun muhimman kayan buƙatun rayuwa, kamar abinci da ruwan sha ba.
Hukumomi sun yi gargaɗin cewa man fetur ɗin da ake da shi a Zirin Gaza, zai iya ƙarewa a cikin sa'a 24 zuwa 72.
Hukumar ayyukan jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargaɗin cewa man fetur ɗin da ake da shi ba zai wuce kwanaki ƙalilan ba.
Ko kafin taƙaita al'amura a baya-bayan nan, mazaunan Gaza tuni suke fama da tsananin ƙarancin abinci da taƙaita zirga-zirga da kuma ƙarancin ruwan sha.
- Rikicin Gaza: 'Ban taba zaton zan rayu ba'
A ranar Litinin, ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce za su ƙaƙaba wani matakin "datse komai gaba ɗaya" a yankin.
"Ba lantarki, babu ruwan sha, babu iskar gas - duka za a datse SU," in ji shi, ya ƙara da cewa "muna faɗa da dabbobi ne kuma za mu ɗauki mataki gwargwado."
Ministan samar da ababen more rayuwa na Isra'ila daga bisani ya ba da umarnin katse ruwan sha zuwa Gaza nan take, yana cewa: "Abin da aka saba yi a baya, ba za a yi shi ba a nan gaba."
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar lafiya ta al'ummar Falasɗinawa ta ce asibitoci na fuskantar ƙarancin magunguna da kayan amfanin asibiti da man fetur saboda matakan Isra'ila.
Ta yi kira ga ƙasashen duniya su buƙaci Isra'ila ta "dawo da hasken lantarki", kuma ta samar da muhimman buƙatun rayuwa kamar magunguna da man fetur da jannaretocin lantarki.
Isra'ila ta ƙaddamar da gagaruman hare-haren ramuwar gayya ta sama a Gaza tun ranar Asabar, inda ta kashe aƙalla mutum 511, tare da jikkata ƙarin 2,750, a cewar ma'aikatar lafiyar Falasɗin.
Daren Lahadi musamman ya ga manyan hare-hare, da yiwuwar su ne mafi girma da Gaza ta yi fama da su a cikin shekaru - gaba ɗaya tsawon daren, an yi ta jin tashe-tashen bam masu ƙarar gaske bi-da-bi a faɗin Zirin.
Yayin da hare-haren suka ci gaba da gudana bayan alfijir, baƙin hayaƙi ya mamaye sararin samaniya, kuma ana iya jin ɗanɗanon ƙurar gine-ginen da suka ruguje a cikin iska.
Wasu daga cikin hare-haren, an kai su ne a yankin kan iyaka da ke gabashin Gaza, daga inda mayaƙan Hamas suka ƙaddamar da hare-harensu da safiyar Asabar.
Ga alama Isra'ila tana kai farmaki kan waɗannan yankuna ne, daidai lokacin da take ƙoƙarin haɓaka matakan tsaro a can.
Akwai kuma rahotanni daga shaidu da ke cewa Isra'ila na amfani da makaman atilare a yankin kan iyaka.
Isra'ila ta ce tana kai hare-hare ne kan tungogin Hamas ne a Gaza, sai dai akwai rahotannin da ke cewa ana far wa fararen hula.
Ma'aikatar harkokin wajen Falasɗin ta ce hare-haren Isra'ila sun auka wa sansanonin 'yan gudun hijira guda biyu a Gaza - Al-Shati (wanda ake kira sansanin bakin teku) da kuma sansanin Jabalia - inda rahotanni suka ce, an jikkata mutane da dama, wasu kuma sun rasu.
Wani bidiyo da aka yaɗa a intanet daga Jabalia, ya nuna hargitsewar al'amura sosai, ciki har da wata gawar mutum da ake ƙoƙarin ɗaukewa da kuma wani mutum wanda ƙura da jini suka lullube jikinsa.
Ma'aikatar harkokin wajen ta kuma ce hare-haren ta sama sun samu wata makaranta ta Majalisar Dinkin Duniya a Gaza, wadda ke tsugunnar da ɗaruruwan fararen hula ciki har da ƙananan yara da tsofaffi.
- An yi ganawar tarihi tsakanin Isra'ila da Falasdinu
- Yadda zaman fargaba ke karuwa a Yammacin Kogin Jordan