Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ɗangote da Bill Gates na ziyara a Jamhuriyar Nijar da Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran dake faruwa a Najeriya da sauran sassan ƙasashe

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Ɗangote da Bill Gates na ziyara a Jamhuriyar Nijar da Najeriya

    Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya gana da shugaban Gidauniyar Bill and Melinda Gates, wato hamshaƙin attajirin nan na duniya, Bill Gates, da kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ranar Litinin a birnin Niamey,

    Mista Gates da takwaransa na Afirka Dangote sun kai ziyara Jamhuriyar Nijar da Najeriya ne domin ganawa da shugabannin ƙasashen da kuma abokan hulda game da ƙalubalen harkokin kula da lafiya da ci gaban ƙasa.

    Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun rawaito cewa attajiran biyu sun gana da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a Abuja, bayan sun bar birnin Niamey duk dai a ranar Litinin.

    Rrahotannin sun ambato sanarwar da gidauniyar Bill Gates ta fitar ranar Litinin na cewa ziyarar na cikin kudurin attajirin duniyar na yin aiki kafada da kafada da al’ummomi da shugabannin ƙasashe don tallafa wa kirkire-kirkire da za su iya taimakawa wajen hanzarta ci gaba da inganta rayuwa a fadin Afirka.

  2. Airtel ya ƙaddamar da tsarin sadarwar intanet na 5G

    Kamfanin sadarwa na AirtelNigeria ya ƙaddamar da tsarin sadarwar intanet mai gudun famfalaƙi da aka fi sani da 5G.

    Matakin ya kawo adadin kamfanonin da ke amfani da fasahar zuwa uku, waɗanda suka yi alkawarin isar harkokin sadarwar intanet cikin sauri tare da sake fasalin ayyuka a wasu sassan tattalin arzikin da suka haɗar da bangaren lafiya da aikin gona, da sauransu.

    Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ne ya fara ƙaddamar da tsarin sadarwar intanet ɗin sai kamfanin Mafab ya biyo baya.

    Shugaban sashen kasuwanci na kamfanin AirtelNigeria, Femi Oshinlaja, ya ce za a samar da ayyukan tsarin sadarwar 5G a manyan birane da suka hadar da Abuja da Legas da Ogun da kuma jihar Ribas, inda ya ƙara da cewa daga baya za a faɗaɗa ayyukan zuwa wasu sassan Najeriya.

  3. Tinubu zai tafi Faransa wurin taron harkokin kuɗi na duniya

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai gana da shugabannin kasashen duniya a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni a birnin Paris na kasar Faransa domin yin nazari tare da rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta hada-hadar kudi ta duniya.

    Yarjejeniyar za ta kasance ta fifita ƙasashe masu rauni wajen bayar da tallafi da saka hannun jari sakamakon mummunar tasirin sauyin yanayi, da kuma sakamakon cutar korona.

    Wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar sahawara kan ayyuka na musamman da sadarwa, Dele Alake ya fitar, ta bayyana cewa shugaban zai halarci taron na kwanaki biyu tsakanin 22 da 23 ga watan Yuni, wanda zai duba hanyoyin samar da tallafi ga kasashen da ke fuskantar mawuyacin hali na gajeren lokaci.

    A yayin ziyarar aikin a ranar Alhamis, Shugaba Tinubu da sauran shugabannin duniya za su yi nazari sosai kan farfado da tattalin arzikin ƙasa daga tasirin annobar korona, da ƙaruwar talauci, tare da ƙara samar da ci gaba

    eturn to Abuja on Saturday, june 24.

  4. Ana ce-ce-ku-ce kan yawan mutanen da tsananin zafi ya kashe a Indiya

    Jami'ai a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya na gudanar da bincike kan mutuwar mutane waɗanda ake alaƙantawa da tsananin zafi.

    Tsakanin ranakun Alhamis da Lahadi, an bayar da rahoton mutuwar mutane 68 a gundumar Ballia, mai tazarar kilomita 274 (mil 170) daga babban birnin jihar Lucknow.

    A yanzu gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti da zai duba sanadin mutuwar mutanen.

    Yanayin zafi a sassa da dama na Uttar Pradesh ya kai maki 42c zuwa 47c a cikin makon da ya gabata.

    Gwamnati ta shawarci tsofaffi da su yi zamansu a cikin gida.

    A jihar Bihar mai makwabtaka, kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa sama da mutane 40 ne suka mutu sakamakon zafi tun ranar 31 ga watan Mayu, amma jami'an jihar sun musanta hakan.

    Dokta Umesh Kumar, jami'in da ke kula da dakin kula da bala'o'i na Bihar, ya shaida wa BBC cewa sun samu rahoton mutuwar mutum daya ne kawai sakamakon tsananin zafi, a gundumar Jehanabad.

    An fara ce-ce-ku-ce a Uttar Pradesh a ranar Juma'a bayan Diwakar Singh, shugaban asibitin gundumar Ballia, ya shaida wa manema labarai cewa kusan mutane 25 ne suka mutu, kuma mai yiwuwa zafi ne ya haddasa hakan.

    "Yawancin marasa lafiya sun haura shekaru 60 wadanda dama suna fama da wasu cututtukan tun asali, zafi ya tsananta ciwon kuma an kai su asibiti cikin mawuyacin hali. Sun mutu duk da cewa an ba su isassun magunguna" in ji Dr Singh.

  5. Iraki ta karɓo ɓangorin dutse mai ɗauke da rubutun da aka yi shekara 2,800

    Iraƙi ta baje-kolin wani rubutu da aka sassaƙa a jikin wani ɓangorin dutse tsawon shekara 2,800 bayan ƙasar Italiya ta mayar mata da shi.

    Kusan shekara arba'in dutsen mai ɗumbin tarihi ya shafe a hannun hukumomin Italiya.

    Dutsen na dauke da nau'in rubutun da ake kartawa a jikin dutse - wanda wani tsarin rubutu ne da akan yi a kan yumbu da tsoffin haruffan zamanin Babila.

    Hukumomin Italiya sun miƙa ɓangorin dutsen ga shugaban Iraƙi, Abdul Latif Rashid lokacin da yake wata ziyara a birnin Bologna cikin makon jiya.

    Ba a fayyace yadda aka gano dutsen ba - ko kuma yadda ɓangorin ya je ƙasar Italiya, inda 'yan sanda suka ƙwace shi a shekarun 1980.

    Ministan al'adun ƙasar Iraƙi, Ahmed Badrani ya bayyana cewa, mai yiwuwa an gano shi ne lokacin aikin tonon kufai a madatsar ruwan Mosul da aka gina a daidai lokacin.

    Iraki, wadda galibi ake bayyana ta a matsayin "tushen wayewa", ta yi fice a fannoni da yawa ciki har da, kasancewarta inda aka fara rubutu a tarihin duniya.

    A ƙarshen karni na takwas, Bayt al-Hikmah (Cibiyar Hikima) a ƙasar ta kasance ɗakin littattafan kimiyya da fasaha da lissafi da aikin likitanci da falsafa mafi girma a duniya.

    Wawar kayan tarihin Iraƙi ta yi tsanani bayan mamayar da Amurka ta yi, shekara 20 da ta wuce.

    Shugaban na Iraƙi ya yaba wa haɗin kan da Italiya ta nuna, ya kuma ce zai yi ƙoƙarin ƙwato dukkan kayan tarihin ƙasar daga ƙetare.

  6. Real Madrid ta ɗauki Joselu daga Espanyol

  7. Fafaroma ya yi wa waɗanda aka kashe a Uganda addu'a

    Fafaroma Francis ya jagoranci addu'o'i a fadar Vatican ga waɗanda harin mayaƙan kungiyar IS ya shafa a wata makaranta a Uganda.

    Kimanin mutane 40 - akasarinsu dalibai - aka yi wa kutse, aka harbe sannan aka ƙone su ƙurmus a garin Mpondwe da ke yammacin ƙasar a ranar Juma'a da daddare.

    Haka nan maharan sun yi garkuwa da ɗalibai shida kafin su tsallaka kan iyaka zuwa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.

    Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni ya yi Allah-wadai da harin wanda ya bayyana shi a matsayin gagarumin laifi.

    Iyalan wasu daga cikin waɗanda aka kashe sun fara binne 'yan uwan nasu.

  8. Shirin bayar da bashin karatu ga ɗalibai ba mai ɗorewa ba ne - ASUU

    Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sauya dokar ba da bashin karatu ga dalibai da ya amince da ita, zuwa tallafin karatu domin bai wa ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi damar samun ilmi mai zurfi.

    A wata hira da gidan Talbijin na Channels ranar Lahadi, shugaban ASUU ya ce bashin karatun ba abu ne mai yiwuwa ba. A cewarsa, bayar da bashi don yin karatu "ba zai dore ba".

    Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce, “tunanin bayar da bashin karatu ga dalibai ya zo ne a 1972 kuma yana cikin harkokin bankuna da aka kafa".

    Ya yi iƙirarin cewa mutanen da suka karɓi bashin, ba su taɓa biya ba, kuna iya zuwa ku bincika. A shekarar 1994 ko 1993, sojoji sun kafa dokar soja mai lamba inbda suka kafa hukumar bayar da bashi ga ɗalibai. Sai Majalisar dokoki ta daidaita ta a shekara ta 2004 kuma a cikin shekara ɗaya, ta wargaje. Kuɗaɗen suka bace. Muna so mu ga yadda wannan zai bambanta".

    A cewarsa, akwai dalibai sama da miliyan daya a jami’o’in gwamnatin Najeriya kuma rancen ba zai iya biyan kudin karatun dalibai ba.

    A ranar Litinin ne Shugaba Tinubu ya sa hannu a kan dokar ba da bashi ga dalibai domin cika alƙawarin da ya dauka a lokacin yaƙin neman zabensa.

    Shugaban majalisar wakilai ta 9, Femi Gbajabiamila, wanda yanzu shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ne ya dauki nauyin gabatar da ƙudurin dokar a majalisa.

    Dokar ta tanadi ba da bashi maras ruwa ga daliba masu ƙaramin ƙarfi a Najeriya.

  9. Kalli bayani kan falalar kwanaki goma na farkon watan Dhul-Hijjah

  10. An buƙaci wasu maniyyatan Abuja su koma gida

    Wasu maniyyata aikin hajji a Najeriya, sun koka dangane da yadda aka umarci wasunsu, su koma gida, saboda ba za su samu damar zuwa aikin hajjin bana ba, duk kuwa da biyan kuɗin aikin hajjin ta hanyar adashin gata.

    Maniyyatan sun ce hakan ya faru ne bayan sun kwashe makonni a sansanin mahajjata na Abuja.

    Daya daga cikin maniyattan da lamarin ya shafa ta bayyana wa BBC Hausa cewa ta share fiye da kwanaki goma a sasanin alhazan babban birnin na Najeriya, amma har yanzu ba ta san makomarsu ba, sakamakon rashin wani bayani daga bangren mahukunta.

    "Ga shi muna zaune ba su yi magana ba, na fara magana sai aka yanke waya, an ce min na yi hakuri na wuce gida,"

    "Shi ne na ce me ya faru da za ka ce na wuce gida bayan na zauna sati uku, kuma sai a ce min na wuce gida, mene ne ya faru? Daga nan sai ya yanke waya."

    "Idan gwamnati za ta taimake mu, muna so, tunda ga shi dai dukkanmu ba mu wuce ba, muna da yawa da maza da mata.

    A wani taƙaitacan labari da darekta a hukumar alhazan Najeriya, Abdullahi Magaji Harɗawa ya yi wa BBC Hausa, ya ce maniyyatan da ke wannan koke sun fito ne ba tare da an kira su ba.

    Sai dai ya ce hukumar alhazan na ɗaukan mataki.

    "Alhazai ne waɗanda suka yi rajista ƙarƙashin 'tour operators', akwai jirginsu da aka ɗaukar musu na musamman wanda zai yi jigilar su."

    "kamfanin da aka fara da su, sun zo sun fara kuma sun gaza, amma yanzu ana shirya wani jirgin da zai zo ya kwashe su."

    "Kowane jirgi akwai lokacin da yake tashi, saboda da haka idan wasu sun zo ba tare da an kira su ba, wannan su suka kawo kan su."

    Ya kuma yi alƙawarin cewa za su tabbatar cewa an kwashe dukkanin alhazan zuwa Saudiyya.

  11. Yadda ya kamata a kula da yara masu sikila a lokacin damuna

    Yau ce ranar faɗakarwa kan cutar sikila ta duniya.

    Ga bayani dalla-dalla kan yadda za a kula da yara masu fama da cutar a lokacin damina, daga bakin Hajiya Badiyya Inuwa, wata mai gidauniyar kula da masu cutar a Najeriya.

  12. Ƴan bindiga sun yashe gidan jakadan Tunisiya a Sudan

    Wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai a babban birnin kasar Sudan, Khartoum, wawushe kayan da ke a gidan jakadan Tunisiya a Sudan, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Tunisiya ta tabbatar a ranar Lahadi.

    Ma'aikatar harkokin wajen ta bayyana lamarin a matsayin "babban cin zarafi ga yarjejeniyar huldar diflomasiyya, da kuma keta alfarmar babban ofisoshin jakadanci."

    Ma'aikatar ta yi kira da a binciki wadanda suka aikata wannan ɓarna, sannan kuma suka yi kira da a kawo karshen fadan na Sudan da aka fara a watan Afrilu.

    Tun bayan ɓarkewar faɗan a cikin watan Afrilu, an kai farmaki kan ofisoshin jakadanci wasu ƙasashe da ke a birnin Khartoum, ciki har da na Qatar, da Kuwait, da Libya, da Jordan da kuma Oman.

  13. Shugaban Uganda ya tura ƙarin dakaru a yankin da aka kashe mutane 40

    Shugaban ƙasar Uganda, Yoweri Museveni ya bayar da umarnin tura ƙarin dakaru zuwa yammacin kasar bayan wani mummunan hari da aka kai a wata makaranta ranar Juma'a.

    Mutane 40 ne suka mutu sakamakon harin da aka kai a Mpundwe da ke kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango, kuma yawancinsu ƙananan yara ne.

    Ana zargin mayakan da ke da alaka da kungiyar IS da sunan kungiyar Allied Democratic Forces da kai harin.

    Babu tabbas kan dalilin da ya sa aka kai wa makarantar farmaki.

  14. Shugaban Uganda ya warke daga cutar korona

    Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya ce a yanzu ya warke daga cutar korona wadda ya yi fama da ita.

    Kwanaki goma sha ɗaya bayan kamuwa da cutar, Mista Museveni ya ce a yanzu shi "jarumi ne wanda ya kammala yaƙi da cutar ta Covid-19".

    A ranar 7 ga watan Yuni ne ya bayyana wa al'umma cewa ya kamu da cutar korona - lamarin da ya haifar da muhawara da ce-ce-ku-ce sosai a yankin gabashin Afirka.

    A ranar Lahadin da ta gabata, ya bayar da sanarwa a cikin wani dogon bayani a shafinsa na Twitter, cewa ya warke daga cutar.

    Ya bukaci 'yan Uganda da su bi dabarun kiwon lafiya ta hanyar guje wa abubuwan da ke haifar da hadari kamar shan taba da barasa, su kuma rinƙa motsa jiki da cin abinci mai kyau..

    Duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana cewa korona ta fita daga cikin jerin cutuka da ke barazana ga al'umma, har yanzu cutar na ci gaba da yin illa a ɓangarori daban-daban na duniya.

  15. Ƙungiyar ƙwadago za ta sake ganawa da gwamnatin Najeriya kan cire tallafi

    Manyan ƙungiyoyin ƙwadago biyu a Najeriya za su gana da jami'an gwamnati don kokarin ganin sun amince da sabon mafi karancin albashi da kuma wasu bukatu na ma’aikata bayan da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur.

    Janye tallafin ya jawo tashin farashin mai da tsadar sufuri.

    Ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Najeriya ta ce yau ne wa'adin da ta ba gwamnatin tarayya ke cika, kan bukatarta mayar da mafi karanci albashi naira dubu 200 sakamakon janye tallafin mai.

    Ƙungiyar ta ce bukatar biyan mafi kakantar albashin naira dubu 200 na cikin bukatun da ta mika wa gwamnatin Tarayya, domin ragewa ma'aikata raɗaɗin wahalar janye tallafin mai da sabuwar gwamnatin ta yi.

    Comrade Nuhu Toro, sakatare janarar da kungiyar ya faɗawa BBC cewa suna kan bakansu akan albashi mafi ƙanƙanta na naira dubu 200 wa ƙaramin ma'aikaci a Najeriya domin tsadar rayuwar da mutane suka shiga.

    Ya ce "Farashin kayayyaki da rayuwa ma gaba daya tsada ya keyi, saboda haka gwamnati ba ta da hujja illa ta ƙara ma ma'aikata mafi ƙanƙantar albashi na naira dubu 200 domin su ma'aikata su suke ƙirƙirowa ta arzikin ƙasa".

    "Gwamnati za ta iya biyan wannan albashin idan ta rage almubazaranci, idan ta rage sama da faɗi da dukiyan talakawa, kuma idan ta rage kashe kuɗi a kan abubuwan da bai kamata ba."

    Toro ya dai ƙara da cewa dole ne gwamnati ta rage yawan kashe kudin da take yi, shi ne za ta sami yanda za tayi ta biya ma'aikata albashi mafi ƙanƙanta naira dubu 200.

  16. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi Aisha Babangida ce ke fatan an tashi lafiya tare da fatan kasancewa da ku a wannan rana ta Litinin.

    Za mu kawo muku labarai da rahotanni iri-iri daga sassan duniya.

    Sai ku kasance da mu.