Babu wanda APC ta bai wa shaidar zama shugabanta a Kano da Sokoto

Asalin hoton, @BuniMedia
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayar da takardar shaidar cin zabe ga shugabanninta na dukkan jihohin kasar amma ban da jihar Kano da Sokoto.
Sakataren jam'iyyar, John James Akpan Udo-Edehe ne ya mika takardar shaidar cin zaben ranar Alhamis yayin wani takaitaccen taro da aka gudanar sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Lamarin na zuwa ne bayan kusan wata huɗu da aiwatar da zaɓukan shugabannin a matakin jihohi, waɗanda suka haifar da ɓangarori a cikin jam'iyyar daban-daban.
Tun da sanyin safiya ne aka jibge jami'an tsaro a ciki da kewayen sakatariyar jam'iyyar.
Daga cikin jihohin da suke fama da rikici akwai Kano da Kebbi da Zamfara da Bauchi da Kwara da Osun da Delta da Rivers.
Sai dai an bai wa shugabannin dukkan jihohin da suke fama da rikici idan ban da jihar Kano da Sokoto.
Hasalima ba a ga fuskokin Abdullahi Abba da Ahmadu Haruna Zago, mutanen da ke ikirarin shugabancin jam'iyyar na jihar Kano, a wurin taron ba.
Jihohin da ke cikin rikici

Asalin hoton, BBC
A wasu jihohin kamar Kano, ɓangaren da ke samun goyon bayan Sanata Ibrahim Shekarau ya zaɓi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaba, yayin da ɓangaren Gwamna Abdullahi Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas.
Sai dai a ƙarar da ɓangaren Ganduje ya shigar bayan kammala zaɓen na watan Oktoban 2021, wata Kotun Tarayya ta ayyana ɓangaren Sanata Shekarau a matsayin waɗanda suka yi sahihin zaɓe kuma ta bayyana Ɗan-Zago a matsayin halastaccen shugaba. Kodayake ɓangaren gwamnan ya ɗaukaka ƙara.
A Jihar Kebbi ma haka lamarin yake, inda ɓangaren tsohon gwamna kuma sanata mai-ci, Muhammadu Adamu Aleiro, ya buɗe wata sabuwar hedikwatar jam'iyyar.
Hakan kuwa na faruwa ne duk da ƙoƙarin sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangarensa da na gwamnan jihar, Sanata Atiku Bagudu da kwamitin Abdullahi Adamu ya yi.
Bangaren Gwamna Bagudu dai ya bayyana buɗe sabon ofishin a zaman haramtacce wanda aka yi ba bisa doka ba.











