UNGA76: Abu uku da Buhari ya fada wa shugabannin duniya a taron MDD

Asalin hoton, BashirAhmed
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida cewa yana samun nasara a kokarin murkushe mayakan Boko haram da suka addabi yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Buhari ya shaida hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a gaban shugabannin duniya sama da 80 da ke halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76 a Birnin New York na Amurka.
Shugaban ya ce babu shakka Najeriya da sauran kasashen yankin Tafkin Chadi na samun nasara wajen yakar Boko haram da sauran kungiyoyin jihadi sai dai akwai bukatar sake kara kaimi.
Jawabin Shugaban na kusan sa'a guda ya tabo batutuwa da dama kama daga batun tsaro, yaki da annobar korona da matsalolin sauyin yanayi da hakkin bil adama.
Taken taron na wannan shekara, shi ne ' Gina jajircewa ta hanyar kyakkyawan fata- Don murmurewa daga annobar Korona, sake gina wani tsari mai ɗorewa, duba bukatun duniya, girmama hakkokin jama'a, da kuma kara wa majalisar dinkin duniya kuzari'.
Tsaro

Asalin hoton, BashirAhmed
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce daga cikin batutuwan da ke addabar kasashen Afirka da haifar da nakasu a kokarin yakar mayakan jihadi da sauran matsalolin tsaro shi ne batun yaduwar kananan makami a duniya.
Buhari ya ce Najeriya da sauran kasashen Afika na goyon-bayan samar da tsari da dokokin da za su yaki yaduwar makamai, domin haka zai taimaka a yakin da kasashen Afirka ke yi da ta'addanci.
Ya ce duk da cewa suna samun nasara a yaki da Boko Haram a arewa maso gabashi, da tafkin chadi da kuma 'yan bindiga a yankunan arewa maso yammaci da tsakiya, Najeriya za ta ci gaba da aiki da sashin yaƙi da ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya domin murkushe 'yan ta'adda.
Sannan ya ce suna goyon-bayan kasashen duniya kan batun takaita mallakar makamin Nukiliya.
Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa tayi kokari wajen ganin ta kawo karshen ayyukan ta'addanci da kawar da mayakan Boko Haram, kuma a wannan lokaci suna ganin nasara a arewa maso gabashin kasar da kuma sauran yankunan Tafkin Chadi.
Annobar Korona

Asalin hoton, BashirAhmed
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ta taka rawar gani a yaki da annobar korona musamman saboda irin gudunmawar da suka rinka samu daga sauran kasashen duniya.
Ya kuma ce an samar da manyan dakunan gwaji hudu da kayan aikin zamani, sannan ya shaida cewa gwamnati ta dau daruruwan ma'aikatan lafiya domin bada taimakon kawar da cutar.
Shugaban ya kuma ce a yanzu babban abin da suka sanya gaba shi ne kokarin kawar da ba da kariya daga kamuwa da sabon nau'in annobar na Delta.
Ya kuma yi kira ga manyan kasashen duniya su yi adalci wajen rabon rigakafin annobar korona musamman tsakanin kananan kasashe.
Ya kuma roki kasashen da ke bin Najeriya basusuka su sake basu lokaci ko yafe musu la'akari da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki saboda tasiri annobar korona da matsalolin tsaro.
Dimokuradiya

Asalin hoton, BashirAhmed
Shugaba Buhari ya ce duk da tarin matsalolin Afirka musamman tsaro, akwai wasu abubuwan da bai kamata a kawar da ido a kansu ba.
Shugaban ya jero batun rashin shugabanci nagari da baya kan turbar dimokuradiya da keta hakkin bil'adama da talauci da rashin adalci da daidaito a matsayin manyan batutunwan da ke bukatar a duba.
Ya ce "Babu matsalar da maganceta ke zuwa cikin sauki, dole akwai tsari irin na dogon-zango da kuma samun hadin-kai daga kasashen duniya wanda zai yi tasiri".
Sanna ya ce kyawawan ayyukan dimokuradiyyar da ake gani a Afirka ta yamma na disashewa saboda shugabannin Afirka masu naci da kwadayin Mulki. Ya ba da misali da abin da ya faru a Mali da Guniea.
Shugaba Buhari ya kuma jaddada Najeriya na goyon bayan kasashen Afirka da yankin yammacin Afirka na shawo kan irin wadanan matsaloli.
A karshe ya jaddada cewa Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Majalisar Dinkin Duniya cimma burinta na dakile matsalolin sauyin yanayi.











