Mutumin da ya hau bene a keken guragu domin taimaka wa jama’a
Lai Chi-Wai gwani ne wajen hawa dogayen gine-gine sai dai ya samun shanyewar jiki sakamakon hatsarin mota shekaru goma da suka gabata.
Amma duk da wannan nakasa da yake fama da ita, ya hau ginin Nina towers da ke Japan domin ya ja hankalin jama'a wajen tara kudi ga masu larurar laka.
Ya tara $670,000 inda yake so a yi amfani da su wajen yi mus magani.
Ya ce wannan bajinta tasa tana sa wa yana mantawa cewa shi mai larurar nakasa ne.