Sojojin Kamaru sun kashe wasu 'yan awaren yankin renon Ingila

Sojojin Kamaru

Jami'an tsaro a Kamaru sun ce sun kashe wasu masu tada-kayar-baya 17 tare da cafke mutum 7 da ke dauke da wasu kayan fashewa a yankin renon Ingila.

Jami'an sun kai farmakin ne karkashi atisayen ''Operation Boyo 1" wanda ya ba su damar kwashe kwanaki 6 a cikin daji suna bin takun 'yan aware da ke kai farmaki a kan jama'a.

Kusan sojoji 450 ne ma'aikatar tsaro ta tura daji inda suka rinka hawa tsaunuka da tafiya cikin ruwa kana kuma suka rinka nitsewa a cikin tabo da zummar mayar da tsaro da zaman lafiya a yankin renon Ingila.

A wannan karon ne dai jami'an tsaron suka samu nasarar dawowa da dumbin ganima kamar makamai da wasu tarin kayayyaki da ma masu masu fafutukar mutum bakwai.

Kwamandan shiyya ta 51 na rundunar sojin kasar, ya ce wannan kadan ne daga cikin daga cikin irin kayayyakin da jami'ansu suka tattaro a yayin farmakin da suka kai.

Ya ce a yayin farmakin sun yi karo da sansanoni na masu fafutkar da dama.

Sojojin Kamaru

Sakamakon wannan nasara da sojojin suka samu a kan masu fafutukar, hukumomi suka yi kira ga jama'a da su rinka ba su hadin kai domin kai wa ga irin wadannan mutane masu fafutuka a duk inda suke.

A yanzu haka dai, mahukuntan sun umarci iyaye da su mayar da 'ya'yansu makarantu daga ranar 5 ga watan Oktoba da ke tafe.