Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Katsina: 'Yadda aka kashe maigidanmu aka bar mana marayu 15 a Batsari'
Latsa alamar lasifika da ake sama domin sauraren hirar da Aisha Shariff Baffa da wata da aka kashe mijinta
Daya daga cikin matan da aka kashewa mazajensu a yankin Batsari na Katsina a Najeriya ta bayyana wa BBC irin mawuyacin halin da suka shiga tun bayan da 'yan bindiga suka kashe maigidansu.
Matar ta ce su uku ne mijinsu ya bari da kuma 'ya'ya 15, kuma a yanzu haka suna samun mafaka a cikin garin Batsari inda suke fafutukar abin da za suci su da yaransu
Tun da farko a hirar da BBC ta fara yi da Sarkin Ruman Katsina, Hakimin Batsari Alhaji Tukur Mu'azu Ruma ya bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe fiye daruruwan magidanta a karamar hukumarsa tare da barin zawarawa fiye da 600 da marayu fiye da 2000.
Sannan ya ce kusan kashi daya cikin uku na mutanen masarautarsa sun zama 'yan gudun hijira inda suka warwatsu a jihohi makwabta da sauran sassan Najeriya.
Basaraken ya ce yankinsa na cikin wani matsanancin hali na matukar bukatar agajin gwamnati da masu hannu da shuni, duk da ya ce gwamnati na ciyar da mutanen da ke gudun hijira a wani sansani.