'Na aurar da 'ya'yana da kiwon akuya'

Latsa hoton da ke sama domin kallo

Ba kasafai ake samun mutanen da dabbobi ke zamo musu silar arziki ba, amma ga Malama Dudu Adamu Gantsa labarin ba haka yake ba.

Ta ce lokacin da aka ba ta dabbobin guda uku ba ta zaci arzikinta aka ba ta ba, inda yanzu haka dabbobin suka tashi da uku zuwa fiye da 20 bayan shekara daya.

Daga wadannan dabbobi nake ciyar da 'ya'yana wadanda marayu ne sannan kuma nake yi musu aure da ma karatunsu.

Dudu ta bugi kirjin cewa "ba karamin ma'aikaci ba, ko ma'aikatan fedaral za su zuba tunda wasu kan je wurinta rance kafin wata ya kare.