Yadda aka yi garkuwa da hakimin Birnin Gwari

Hakimin Birnin Gwari

Asalin hoton, OTHERS

Rahotanni na cewa wasu 'yan bindiga da ba tantance su ba sun yi awon gaba da hakimin garin Birnin Gwari a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwarin.

An dai ce da misalin karfe 12 na ranar Laraba ne aka yi garkuwa da Alhaji Ibrahim Yahaya a kan hanyarsa ta zuwa wani wuri da aka kebe domin yin sasanci tsakanin al'ummar Birnin na Gwari da masu sata da kisan jama'a a yankin.

A kwanakin baya an yi wata tattaunawar tsagaita wuta tsakanin 'yan bindiga da jami'an karamar hukumar Birnin Gwari karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar, Alhaji Garba Gambo.

Sai dai an cimma yarjejeniyar ce ba tare da karbe makaman da ke hannun 'yan bingidar ba.

Kuma wasu bangarorin 'yan bindigar sun bayyana karara cewa ba za su kasance cikin yarjejeniyar ba.

Bayanai daga mazauna yankin na nuna cewa 'yan bindigar na shawagi firi-falo da makamansu a cikin kauyuka suna gudanar da harkokinsu ba tare da shakku ko fargaba ba.