Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda muka san akwai barayi dubu goma a Zamfara'- Gwamnatin Zamfara
Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren hirar da Mustapha Musa Kaita ya yi da Ibrahim Dosara
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa akwai barayin shanu da kuma 'yan bindiga a kalla 10,000 da ke cin karansu ba babbaka a jihar.
Tun bayan da gwamnatin ta bayyana wannan kididdigar, tuni jama'a suka fara cece-kuce kan yadda aka samu wannan kididdigar.
BBC ta tuntubi mai magana da yawun gwamnan jihar ta Zamfara Ibrahim Dosara ta wayar tarho inda aka fara tambayarshi ko ya aka yi suka samu wannan kididdigar?
Dosara ya bayyana cewa sun samu wannnan kididdiga ta hanyar jami'an tsaro masu tattara bayanan sirri, da kuma 'yan kato da gora da suke aiki tare dasu.
Ya bayyana cewa akwai kungiyoyi na daba a kalla guda takwas a jihar ta Zamfara.
Kamar yadda ya bayyana, ''akwai dabobi na 'yan ta'adda da ke dajin Dumburu , akwai kuma dabobi da ke bangare na bakalori a bayan ruwa , da kuma na dajin 'Dan sadau, da na dajin Anka , da na dazukkan Maru da sassan Bungudu, su ne suka taru suka bada wannan kididdiga.''
'Me yasa kuna da wadannan bayanan kuma baku yi maganinsu ba?'
A tattaunawar da BBC ta yi da mai magana da yawun gwamnan, an tambaye shi ko me yasa suna da irin wadannan bayanai kuma basu yi maganin 'yan dabar ba inda ya bayyana cewa:
''Abu ne na yaki, wanda ake bukatar dabaru na yin yaki da wadannan mutanen.''
A cewarsa 'yan ta'addan suna aiki ne da bayanan da wasu mutanen da ke cikin al'umma ke ba su, alal misali kafin a kai masu hari sai su kauracewa yankin saboda bayanan da suke da su.
Ya kuma bayyana cewa barayin suna da makamai fiye da wadanda jami'an tsaro suke da su.
''Suna samun makaman su daga wasu sassan yammacin Afirka ,'' inji shi.
Jihar Zamfara na cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar rashin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma satar shanu.
Sai dai a kullum gwamnatin kasar na ikirarin tura rundunoni na jami'an sojoji domin dakile matsalolin da ke yankin amma hakan bai hana kai hare-haren ba.
A karshe ya fada cewa yakamata a jinjina wa Gwamnatin Jihar Zamfara saboda irin kokarin da ta ke yi wajen dakile wadanan 'yan ta'adan domin kawo karshen tashin hankalin da al'ummar Zamfara ta ke ciki.