Kalli bidiyon Paul Pogba a Ka'aba
Dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba ya sake gudanar da aikin Umarah a bana, inda yace ya ji dadin zuwa dakin Allah.
A bara ma Pogba ya je umarah har ma ya gana da babban limamin masallacin Madina Shaikh Ali Bin Abdurrahman Khuzaifi.
Pogba ya je kasa mai tsarkin ne makwanni kadan kafin a fara Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Rasha a watan gobe.