Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
ADIKON ZAMANI: Kun san babban ƙalubalen da mata ke fuskanta a siyasa?
A filinmu na Adokon Zamani na wannan makon, mun kawo tattaunawa ta musamman kan irin ƙalubalen da mata ke fuskanta a harkokin siyasa.
Filin ya tattauna da Binta Masi Garba, 'yar majalisar dattawan Najeriya, da Hajiya Rabi Abdullahi, jami'a a kungiyar mata ta WRAPA da kuma Isma'il Ahmad, shugaban matasa na jam'iyyar APC mai mulkin kasar.