ADIKON ZAMANI: Kun san babban ƙalubalen da mata ke fuskanta a siyasa?

Bayanan sautiKu saurari shirinmu na Adikon Zamani na wannan makon

A filinmu na Adokon Zamani na wannan makon, mun kawo tattaunawa ta musamman kan irin ƙalubalen da mata ke fuskanta a harkokin siyasa.

Filin ya tattauna da Binta Masi Garba, 'yar majalisar dattawan Najeriya, da Hajiya Rabi Abdullahi, jami'a a kungiyar mata ta WRAPA da kuma Isma'il Ahmad, shugaban matasa na jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

Sanata Binta Masi

Asalin hoton, TWITTER

Bayanan hoto, Sanata Binta Masi ta ce mata za su kawo sauyi sosai a siyasa