Yadda zabtarewar ƙasa sakamakon ruwan sama ta kashe mutum fiye da 200 a Ethiopia

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Yadda zabtarewar ƙasa sakamakon ruwan sama ta kashe mutum fiye da 200 a Ethiopia

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon zaftarewar ƙasa a Habasha sun ƙaru zuwa 229.

Jami'ai a gundumar Gofa sun faɗa wa BBC cewa ana cigaba da aikin ceto, amma ana fargabar adadin zai iya ƙaruwa.

Tuni aka kai waɗanda suka tsira da rayukansu asibiti.

Bala'in ya faru ne a yanki da ke aka saba fuskantar zaftarewar ƙasa da damina, kuma wannan ne mafi girma da aka taɓa gani a yankin kusurwar Afirka baki ɗaya.