'Sun kwashe komai na gidana tare da ɗaiɗaita garinmu'

Bayanan bidiyo, Rahoto kan Sudan
'Sun kwashe komai na gidana tare da ɗaiɗaita garinmu'

Ƙasar Sudan na fama da mummunan yanayin yaƙi da ya ta'azzara ayyukan jin ƙai, lamarin da ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, yayin da wasu da dama ke fuskantar barazanar faɗawa ƙangin yunwa.

Wannan na zuwa ne sakamakon yaƙin basasa da ake gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF tun cikin watan Afrilun shekarar da ta gabata.

Babban birnin ƙasar, Khartoum, inda yaƙin ya soma ɓarkewa, har yanzu na fuskantar musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu.

Karon farko tun bayan fara yaƙin wakilin BBC, Mohanad Hashim ya je ƙasar inda ya ziyarci gidansa da na dangi domin ganin halin da Omdurman bayan jerin munanan hare-hare.