Tun bayan ambaliyar Maiduguri 'ruwa kawai nake sha in shayar da jaririna'

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
Tun bayan ambaliyar Maiduguri 'ruwa kawai nake sha in shayar da jaririna'

Wata mahaifiya da ambaliyar Maiduguri ta ritsa da ita, ta ce suna matuƙar buƙatar abinci a sansanin Bakassi da aka ajiye su.

Falmata Goni ta ce ta kuɓuta daga gidansu wanda ruwa ya cinye tare da ƴaƴanta bakwai, kafin hukumomi su kwaso su a mota.

Mahaifiyar wadda ga alama tana cikin halin kaɗuwa ta ce ba ta iya samun abinci sai dai kawai ta sha ruwa kuma a hakan ta shayar da jaririnta.

A cewarta, sauran ƴaƴan nata na samun abin da suke ci ne daga ɗan tallafin da suka samu a maƙwabta.

Hukumomi a jihar Borno sun ce mutane kimanin miliyan biyu ne ambaliyar ruwan ta shafa a birnin Maiduguri.