Kalli yadda aka yi wa ɗalibi dukan kawo wuƙa saboda cin burodi fiye da kima

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Kalli yadda aka yi wa ɗalibi dukan kawo wuƙa saboda cin burodi fiye da kima

An yi wa Caleb Mwangi dukan kawo wuka a makarantarsu da ke Kenya bayan ya ɗebi abinci fiye da kasonsa a lokacin karin kumallo, har sai da ya yi dogon suma, kuma ya shafe kwana 11 a gadon asibiti.

"Lokacin da na isa wurin, ba zai iya sauka daga gadonsa ba, ba ya iya magana," mahaifinsa Fred Mwangi ya shaida wa BBC.