Daga leburanci zuwa gasar Olympics: Rayuwar ɗan Najeriya Anuoluwapo Opeyori

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Daga leburanci zuwa gasar Olympics: Rayuwar ɗan Najeriya Anuoluwapo Opeyori

Anuoluwa, wanda aka haifa a unguwar marasa galihu da ake kira Mokoko a jihar Legas, inda bai samu arziƙin yion wasan badminton a filin mai kyau ba, yanzu zai wakilci Najeriya a gasar Olympics.

Shi ne matashin da ya fi kowane ɗan wasan badminton a nahiyar Afirka lashe kofuna na gasa ta ƙasa da ƙasa.

A wannan bidiyo duba yadda ya samu wannan nasara da kuma tuntuɓar mahaifiyarsa wadda ita ma ta taɓa yin wasan badminton a baya.