...Daga Bakin Mai Ita tare da Hamza Talle Mai Fata

Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
...Daga Bakin Mai Ita tare da Hamza Talle Mai Fata

A wannan makon muna kawo muku ..Daga Bakin Mai Ita tare da fitaccen ɗan wasan fim ɗin nan na masana'antar Kannywood, Hamza Talle Mai Fata wanda aka fi sani da Na-Habiba.

Jarumin wanda haifaffen birnin Jos ne, ya yi makarantar firamare da sakandire da ma jami'a duka a birnin.

Hamza ya ce a baya idan ya ga ƴan fim ƙyamar su yake yi kafin ya tsunduma cikin sana'ar.

"Ina tsokanar su ina kiran su ƴan nanaye. A lokacin ma ƙanena Haruna Talle Mai Fata yana fim tunda ya ma riga ni. Haka akwai yayana ma Baban Umma Talle Mai Fatan wanda yayana ne."

Fitaccen ɗan wasan Hausar ya ce abubuwa guda biyu ne suka saka ya shiga masana'antar fina-finai ta Kannywood.