Zirkzee na son barin Man United, Maresca ya yi watsi da batun dawo da Disasi

Joshua Zirkzee

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan gaban Manchester United Joshua Zirkzee, mai shekara 24, na ganin ficewa daga ƙungiyar a watan Janairu yana da matuƙar muhimmanci idan har zai samu damar shiga tawagar ƴan wasan ƙasar Netherlands a gasar cin kofin duniya da za a yi a bazara mai zuwa. (Mail Plus)

Kocin Chelsea Enzo Maresca ba zai dawo da ɗan wasan baya na Faransa Axel Disasi, mai shekara 27, cikin ƴan wasansa ba, duk da matsalar raunin da masu tsaron bayan ƙungiyar ke fuskanta. (Sun)

West Ham na sha'awar ɗaukar Joshua Zirkzee daga Manchester United, inda sabon kocinta Nuno Espirito Santo ke neman karfafa yanjwasansa na gaba. (Football Insider)

Ɗan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, shi ma yana neman barin Old Trafford a watan Janairu bayan rahotanni sun bayyana cewa Napoli na Zawarcinsa. (Mirror)

Shi kuwa Harry Maguire, mai shekara 32, yana son ci gaba da zama a Manchester United amma dole ne a rage masa albashi domin tsawaita zamansa a ƙungiyar zuwa bayan ƙarshen kakar wasa ta bana. (Talksport)

Leeds za ta nemi sayen ɗan wasan gefe a watan Janairu bayan da ta fuskanci cikas a yunkurunta na ɗaukar ɗa wasan Fulham da Wales Harry Wilson, mai shekara 28, a bazarar da ta gabata. (Sky Sports)

Tsohon ɗan wasan Leeds Raphinha yana cikin ƴan wasan da Manchester United ke sha'awa bayan da ya taka rawar gani a Barcelona amma farashin ɗan wasan na Brazil, mai shekara 28, zai iya kai wa fam miliyan 120. (Fichajes)

Tsohon kocin Everton Sean Dyche ba ya sha'awar zama kocin Rangers bayan da ƙungiyar ta raba gari da Russell Martin. (Sky Sports)