Ku San Malamanku tare da Malam Abdurrahman Ibrahim Idris

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Ku San Malamanku tare da Malam Abdurrahman Ibrahim Idris

Abdurrahman Ibrahim Idris malamin addinin Musulunci ne da aka haifa a garin Bauchi da ke arewacin Najeriya a shekarar 1982.

Ya yi karatun firamare da sakandare a garin na Bauchi, kafin ya yi digirinsa na farko a Jami'ar Maiduguri, da kuma na biyu a ƙasar Sudan.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, malam Abdurrahman na yin digirin digirgir Jami'ar Musulunci ta Uganda.

Ya yi karatun soro a hannun malamai da dama, ciki har da mahaifinsa Imam Ibrahim Idris, da malam Aliyu Yakubu, da Dr Ja'afar Danbaba.