Tun ina sakandire nake sana'o'i iri-iri - Shugaban Ammasco
Shugaban kamfanin bakin mai na Ammasco, Alhaji Mustapha Ado Muhammad ya ce yana mamaki idan ya ga matashi mai jini a jika ba shi da aikin yi.
Ya kuma yi ƙarin bayani kan ainihin cikakken sunan kamfanin nasa.
Abin da Ammasco ke nu fi shi ne Alhaji Mustapha Ado Muhammad and Company, kamar yadda shugaban kamfanin ya shaida wa BBC.
Alhaji Mustapha ya ce ba zai iya ƙirga yawan sana'o'in da ya yi ba a rayuwarsa.
Ya ce tun yana makarantar sakandire yake gudanar da sana'o'i iri daban-daban domin rufa wa kansa asiri.
Alhaji Mustapha ya yi sana'ar canji a kasuwar Wafa da ke Kano, sannan ya yi sana'ar sayen kayan abinci a kasuwar Dawanau, kafin daga bisani ya koma sana'ar harkar baƙin mai.
Shugaban na Ammasco ya ce a yanzu kamfanin nasa na da ma'aikata fiye da 3,500, wanda kuma wannan wani abin alfahari ne a gare shi.
Ya ce a kullum burinsa shi ne ganin matasa sun samu aikin yi, suna gudanar da sana'o'i domin dogaro da kansu.



