Abu biyar da suka sa zaɓen shugaban Senegal ya ɗauki hankalin duniya

Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
Abu biyar da suka sa zaɓen shugaban Senegal ya ɗauki hankalin duniya

Mutane dai na ta magana kan zaɓen Bassirou Dimoaye Faye, matashi ɗan shekara 44, kuma ɗantakara na gamayyar jam’iyyun adawa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Senegal.

Ya kasance zaɓabɓen shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekarau a nahiyar Afrikan.

Wane abun mamaki kuma shi ne Bassirou bai fi tsawon makonni biyu da fitowa daga gidan yari kafin ya zo ya lashe zaɓe.

Mun duba abubuwa biyar da suka sa zaɓensa ya ɗauki hankalin duniya.