Katafaren Kogin Binuwai na barazanar ƙafewa

Bayanan bidiyo, Katafaren Kogin Binuwai na barazanar ƙafewa
Katafaren Kogin Binuwai na barazanar ƙafewa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Masu jiragen ruwa da masunta a Kogin Binuwai na kokawa kan yadda tasirin sauyin yanayi ke shafar sana’o’insu.

Sauyin na yanayi ya janyo ƙarancin ruwa da kuma toshewar sassan kogin, lamarin da ya haifar da koma-baya a harkokin kasuwanci da aka saba gudanarwa tsakanin Najeriya da Kamaru.

Kogin Binuwai ya kasance wata babbar kafar sufuri tsakanin maƙotan ƙasashen biyu.

Mallam Kabiru Sarki, Sarkin Ruwan karamar hukumar Girei inda kogin ya ratsa, ya shaida wa BBC adadin ruwan kogin ya yi matukar raguwa idan aka kwatanta da shekara 20 da ta gabata.

"A da can, nan inda muke tsaye ruwa ne, amma yanzu kogin ya lalace, babban jirgin ruwa da ake kira baji ya daina zuwa domin babu inda zai tsaya saboda karancin ruwa, in ji Sarkin ruwa.

Ya kara da cewa " A shekarun baya idan ka tashi daga kasar Kamaru zuwa Najeriya wuni daya ne amma yanzu sai ai anyi sati bityu sannan ga mai ya kara tsada".

Sarki Kabiru ya ce kullum gwamnatui na cewa za a yashe kogin amma ba su ga komai ba.

Shi kuma Mallam Sa'idu Abdulkadir Mazawaje shugaban masunta a kogin Binuwai ya ce a shekarun baya, masu kama kifi da jirage sukan kama kamar daro dari zuwa dari biyu na kifi a yini guda amma yanzu ko daro biyu ba su kamawa.

Mazawaje ya ce yashe kogin shi ne zai taimaka wajen gyara harkokin kama kifi da kuma sauran sana'o'i a kogin Binuwai. Tun a shekarar 1975 da aka gina gadar kogin Binuwai ne aka yashe shi, kuma daga nan har a wannan shekarar ta 2022 ba a sake yashe shi ba.