Wace ce ƴar Kim Jong Un, wadda za ta iya gadon mulkinsa?

North Korean leader Kim Jong Un talks with his daughter Kim Ju Ae at a banquet to celebrate the 75th anniversary of the Korean People's Army in Pyongyang, 7 February 2023

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kim Ju Ae ta fara bayyana a cikin al'umma tun a 2022. A wannan hoton ita da mahaifinta, sun halarci liyafar cin abincin dare don tunawa da sojojin asar karo na 75 a watan Fabrairun 2023.
    • Marubuci, Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Hukumar Leken Asirin Koriya ta Kudu, NIS, ta ce karamar 'yar shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ka iya zama mai gadon kujerar mahaifinta. Me muka sani game da rayuwar Kim Ju Ae, ta yaya kuma muke ganin za ta iya gadar mahaifin nata?

Kim Jong Un mutum ne da ke matuar ɓoye iyalinsa, don haka ne ma mutane ƙalilan ne suka son wani abu game da iyalansa.

Hatta matarsa, Ri Sol Ju, ya sirrinta ta har zuwa wani lokaci bayan aurensu, ba ta taɓa fita bainar jama'a ba sai a shekarar 2012.

Kafofin yada labaran Koriya ta Kudu sun ce mista Kim ya auri matar tasa ne a shekarar 2009, kuma suka fara haihuwa a 2010.

Ana tunanin ita ce mahaifiyar Kim Ju Ae, wadda aka haifa shekaru bayan aurensu.

An fara ambatar sunan Kim Ju Ae a bainar jama'a a 2013, a lokacin da wani tsohon ɗan wasan ƙwallon kwandon Amurka Dennis Rodman ya yi wani buraguro mai cike da ce-ce-ku-ce zuwa Koriya ta Arewa.

Rodman ya ce ya kwashe lokaci yana tare da iyalan mista Kim, suna hutawa a gaɓar teku kuma har ya ɗauki 'yarsu, wanda ya kira da suna Ju Ae.

An undated photo released by the official North Korean Central News Agency (KCNA) on 05 January 2024 shows Kim Jong Un and Ju Ae inspecting a missile launcher production facility in an undisclosed location in North Korea

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Kim Jong Un da Kim Ju Ae ke duba wurin samar da makamai masu linzami a wani wuri da ba a bayyana ba a arewacin Koriya ta Arewa a watan Janairun 2024

Hatta kafafen yada labaran Koriya ta Arewa "sun tabbatar da ita a matsayin 'yar Kim Jong Un, ba tare da ambaton sunanta ko shekarunta ba", in ji Fyodor Tertitskiy, wanda ke bincike kan siyasar Koriya ta Arewa a Jami'ar Kookmin da ke birnin Seoul.

"Babu wani abu da jama'a suka sani ," in ji shi. Ya kiyasta shekaraunta daga 10 zuwa sama da hakan.

A cikin wani taron sirrin manema labarai da hukumar leƙen asirin Koriya da Kudu, NIS, ta gudanar a shekarar da ta gabata, ta shaida wa 'yan siyasar Koriya ta Kudu cewa ba a shigar da Kim Ju Ae kowace makaranta ba, a maimakon haka ana koya mata karatu ne a gida.

Hukumar ta ƙara da cewa yarinyar na da sha'awar abubuwa irinsu hawa doki, da ninƙaya da kuma wasan kankara. Daya daga cikin mutanen da suka halarci taron manema labaran ya ce, Kim Jong Un ya gamsu da kwarewarta na hawa doki.

Hukumar NIS ta ce Jim Ae tana da yaya da kuma ƙanne da hukumar ba ta tabbatar da jinsinsu ba, waɗanda ba a taba ganin su a bainar jama'a ba.

Kim Jong Un and Kim Ju Ae visiting the Kwangchon Chicken Farm near Pyongyang, January 2024

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kim Jong Un da Kim Ju Ae sun ziyarci gidan gonar kajinsa a Kwangchon da ke kusa da birnin Pyongyang, a watan Janairun 2024

Bayyanar farko a bainar jama'a

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan Nuwamban 2022, Kim Ju Ae ta fara fitowa a bainar jama'a, lokacin da ta halarci gwajin makami mai linzami tare da mahaifinta, tun daga lokacin ne kuma aka riƙa ganinta tare da shi a wurare daban-daban kama da tarukan soji da waɗanda ba na soji ba.

A baya-bayan nan, an ga mahaifinta na sumbatarta a lokacin bukukuwan sabuwar shekara a filin wasa a birnin Pyongyang ranar 1 ga Mayu.

A watan Disamban da ya gabata, sun halarci wurin harba makami mai linzami samfurin Hwasong-18 na Koriya ta Arewa (ICBM), makami mai linzami mai cin dogon zango mafi girma a wurin ma'ajiyar makaman ƙasar.

Ta kuma kasance tare da shi a lokacin da ƙasar ta harba tauraron ɗan adam na leken asiri na Malligyong-1 a watan Nuwamba. Pyongyang ta yi iƙirarin cewa tauraron zai bai wa Mista Kim taswirar fadar gwamnatin Amurka ta White House.

A watan Fabrairun 2023 gidan rediyon Free Asia ya ba da rahoton cewa gwamnatin Koriya ta Arewa na umurtar duk masu suna Kim Jun Ae a ƙasar, da su sauya sunayensu, tana mai cewa wannan al'ada ce ta ƙasar idan ana batun sunayen 'yan gidan sarauta.

Masu sa ido a Koriya ta Arewa sun lura cewa a yanzu ana kallon Kim Ju Ae a matsayin 'yar da ake girmamawa, maimakon "wadda aka fi so". An keɓance sifar “girmamawa” gare ta a ƙasar.

Shi kuwa Kim Jong Un, an kiransa da ''wanda ake mutuntawa" bayan an tabbatar da matsayinsa na shugaban ƙasa.

Kim Jong Un and Kim Ju Ae discuss North Korea's military reconnaissance satellite programme, May 2023

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kim Jong Un da 'yar tasa Kim Ju Ae a wajen taron tattaunawa kan harba tauraron ɗan'adam da zai taimaka wa shirin sojin ƙasar a watan Mayun 2023.

Wanda zai iya gadarsa?

Koriya ta Arewa ta kasance cikin sirri sosai kuma ba ta bayyana abubuwanta ga duniya, amma me yasa Kim Ju Ae take bayyana tare da mahaifinta a kai-a kai?

An faɗa wa ‘yan Koriya ta Arewa cewa iyalan Kim sun fito ne daga tsarkakkiyar zuri'a, ma’ana su kaɗai ne za su iya jagorantar ƙasar, kuma wasu manazarta sun ce gabatar da ita ga jama’a tun tana ƙarama na iya zama hanyar da shugaban Koriya ta Arewa zai bi don tabbatar da cewa ta kafa kanta, tun kafin ta karɓi mulki.

Babu wata takamammiyar magana kan yiwuwar wanda zai maye gurbin mista Kim, duk ka cewa an yi watsi da jita-jitar da aka yi cewa Kim Jong Un ba shi da lafiya.

Kim Jong Un and Kim Ju Ae viewing a military parade at Kim Il Sung Square to mark the 75th anniversary of the founding of the Korean People's Army (KPA), February 2023

Asalin hoton, KCNA/EPA-EFE/REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Kim Jong Un dad Kim Ju Ae a lokacin faretin soji a dandalin Kim Il Sung, a bikin tunawa da sojojin ƙasar karo 75.

To sai dai wasu na cewa hakan na iya zama wata alama da Kim Jong Un zai nuna wa duniya cewa shi mutum ne mai kula da iyalansa

"A lokacin tsoffin shugabannin ƙasar Kim Jong Il da Kim Il Sung, an yi ta yaɗa farfagandar da ta ja hankali kan rawar da shugaban Koriya ta Arewa zai taka a matsayin mahaifi," in ji Edward Howell, malamin siyasa a jami'ar Oxford kuma kwararre kan harkokin siyasa.

"Don haka ina ganin wannan alamar za ta ci gaba ta hanyar nuna ta tare da mahaifinta a fili."

Tun bayan kafuwar Koriya ta Arewa a shekarar 1948, maza daga dangin Kim ne ke mulkin ƙasar, kuma Kim Ju Ae za ta kasance mace ta farko da za ta jagoranci ƙasar, ida ta gaji mahaifin nata.

Amma "duk da cewa samun jinin Kim yana da matuƙar muhimmanci ga shugabancin Koriya ta Arewa, to sai dai samun wani namiji da ba daga zuri'arsu ba zai fi kyau fiye da jagorancin mace," in ji Howell.

Kim Jong Un and Kim Ju Ae visiting the Kwangchon Chicken Farm near Pyongyang, January 2024

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kim Jong Un tare da Kim Ju Ae a lokacin da suka halarci wani gidan gona a Kwangchon da ke kusa da birnin Pyongyang, a watan Janairun 2024

Ya ce akwai wata mata da ka iya zama mai gadon kujerar Kim Jong Un, wadda kanwarsa ce mai suna Kim Yo Jong, wadda aka fara ambatar sunanta a kafafen yaɗa labaran ƙasar cikin watan Maris ɗin 2014.

Misis Yo ta kasance mai riƙe da babban muƙami a jam'iyya mai mulki ta ƙasar.

"Kasancewa ta fi Kim Ju Ae shekaru, ta fi ta masaniya a harkokin siyasar ƙasar," in ji mista Howell.

Ya ƙara da cewa. "Ko da 'yar ce ko kanwar tasa, dukkansu mata ne, to amma samun zuri'ar Kim shi ne abu muhimmi."

Hukumar Leƙen Asirin Koriya ta Kudu, NIS ta kuma ce duk ana kallonsua matsayin wadanda ''za su iya'' gaje kujerarsa, duk da cewa akwai wasu da yawa.

Kim Jong Un and Kim Ju Ae watch a missile drill at an undisclosed location, March 2023

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kim Jong Un tare da Kim Ju Ae sun kalli gwajin makami mai linzami a wani wuri da ba a bayyana ba cikin watan Maris ɗin 2023.

Fyodor Tertitskiy ya ce Kim Jong Un na "gwada ra'ayin al'umma da manyan 'yan siyasar ƙasar kan wanda zai iya gadarsa'', ta hanyar nuna musu Kim Ju Ae a bainar jama'a, wani abu da yace zai ci gaba da yinsa har sai ta tabbata.

Ya ce ya yi wuri a fara maganar wanda zai gaji mista Kim Jong Un tun yanzu.

"Ya ce idan ya mutu a irin shekarun da mahaifinsa ya mutu, 70 zai zama a 2054. In ma Koriya ta Arewa ta ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin a yanayin da take a yanzu, tabbas al'ummar ƙasar ba za ta kasance kamar yadda take a yanzu ba." in ji shi.

Ya kuma kara da cewa, “ya kamata a lura cewa, akwai bambanci tsakanin karbar daidaiton jinsi da kuma karbar mace a matsayin shugaba,” in ji shi.