'Fatanmu a zaɓen gwamnan jihar Edo'
'Fatanmu a zaɓen gwamnan jihar Edo'
A ranar Asabar 21 ga watan Satumba ne mazauna jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar.
Sama da mutum miliyan biyu ne ke da rajistar zaɓe a jihar mai ƙananan hukumomi 18 da rumfar zaɓe 4,519.
A wannan bidiyon, wasu 'yan asalin arewacin ƙasar mazauna jihar sun bayyana fatansu game da zaɓen.



