Ku San Malamanku tare da Sheikh Usman Abubakar
A cikin shirin Ku San Malamanku na wannan mako mun tattauna da Sheikh Usman Abubakar (Abul Husnain), wanda babban malamin addinin Musulunci ne a birnin Kaduna da ke Najeriya.
An haife shi a wani yanki da ke cikin ƙaramar hukumar Ingawa ta jihar Katsina, kafin mahaifinsa ya dawo jihar Kaduna.
Ya ce ya fara karatun allo a gaban mahaifinsa.
Sheikh Usman Abubakar ya halarci Kwalejin Fasaha, inda ya fara da karatun difloma a fannin akanta, daga bisani kuma ya ƙara da babbar difloma.
Haka kuma, ya halarci Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, inda ya yi digiri na biyu a fannin gudanar da kasuwanci (Business Administration).
Sannan neman ilimi ya kai malamin ƙasar Masar inda ya yi karatu a Jami'ar Azhar.
Daga cikin fitattun malaman da ya yi karatu a gabansu har da Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.



