Ban ce mutane su dauki makami don kare kansu ba, su koyi dabarun kare kai nake nufi — C.G Musa

Asalin hoton, Nigeria Defence Headquaters
Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi karin haske game da kiran da babban hafsan hafsoshin kasar, Janar Christopher Musa, ya yi, cewa jama'a su fara tunanin koyon dabarun kare kansu da aka amince da su a duk fadin duniya.
Ta ce jama'a sun yi wannan kira wata fahimta ta daban, to amma abin da babban jami'in tsaron ke nufin shi ne ba wai mutane su dauki makami su kare kansu ba, a'a yana nufin su koyi abubuwa kamar kokowa da judo da dambe da ninkaya da gudu dama tukin mota da dai sauransu.
Birgediya Janar Tukur Gusau, shi ne daraktan yada labarai na rundunar tsaron Najeriya, ya shaida wa BBC cewa shi babban hafsan tsaron na nufin cewa a matsayinka na adam bai kamata ka zauna haka kawai ba tare da ka koyi wata dabara da za a kare kanka ba.
Ya ce," A misali irin mutanen nan da ketare mutane suna kwace musu waya da yawansu wasunsu basa dauke da makami karfi kawai suke nuna wa jama'a, to irin wannan yanayi ne shi babban hafsan tsaron ke ganin ya kamata mutane su koyi dabarun kansu kamar kokawa da gudu, inda duk wanda ya nuna maka karfi kai ma sai ka ware gwanjinka."
"Maganar a dauki makami ma dokoki na Najeriya ma basu yadda wanda ba shi da hurumin daukar makami su dauka ba, idan kuwa har suka dauki makami to akwai dokar da zata yi aiki a kansu."In ji Janar Tukur Gusau.
Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron Najeriyar, ya ce,"Ya kamata jama'a su sani Janar Chiristopher Musa, bai yi Magana a kan jama'a su kare kansu daga wajen 'yan bindiga ba, maganar da ya yi itace su kare kansu daga wasu abubuwa na yau da kullum."
Ya ce, " Ba koyon kokawa da dambe kawai, yana da kyau mutane ma su koyi kamar ninkaya da hawan bishiya da makamantansu, domin kare kai a matakin farko kafin a samu agaji daga jami'an tsaro ko kuma jama'a."
Janar Tukur Gusau, ya ce akwai wasu kasashen duniya da koyar irin wadannan dabarun ya zama dole kuma hakan ba kasawa ba ne, dole mutane su rinka tashi suna kare kansu da kansu don a kada a yi musu sakiyar da babu ruwa.
Wannan rashin fahimta a game da kalaman babban hafsan hafsoshin tsaron na Najeriya ta samo asali ne bayan da ya shawaraci 'ƴan Najeriya da su laƙanci dabarun kare kai daga haɗurra a matsayin mataki na ko-ta-kwana.
C.G Musa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels a ranar Alhamis 21 ga watan Augustan 2025.
Matsalar tsaro na addabar yankuna da dama na Najeriya, inda masu ɗauke da makamai ke kashe mutane tare da tarwatsa su daga muhallansu.
Duk da cewa hukumomi na cewa suna bakin ƙoƙarinsu, amma lamarin na ci gaba da laƙume ɗaruruwan rayuka a yankunan da ake fama da irin waɗannan tashin-tashina, kamar arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma arewa ta tsakiyar Najeriya.










