Ku San Malamanku tare da Sheikh Ibrahim Muhammad Dahir

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Sheikh Ibrahim Muhammad Dahir
Ku San Malamanku tare da Sheikh Ibrahim Muhammad Dahir

A cikin shirin Ku San Malamanku na wannan mako mun tattauna da Sheikh Ibrahim Muhammad Dahir, malamin addinin Musulunci a garin Lafia a jihar Nasarawa.

An haife shi a garin Lafia na jihar Nasarawa, kuma ya ce ya yi digirinsa na farko da na biyu da difloma duka kan fannin shari’a.

Ya fara karatun allo a garin Lafia a gaban fitaccen malamin addinin musulunci a Lafia marigayi Malam Sarki Imam.