Mene ne kamannin gidan yarin Guantanamo Bay?
Mene ne kamannin gidan yarin Guantanamo Bay?
Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayar da umarnin gina wajen tsare ƴan ci-rani a tsibirin Guantanamo, wanda ya ce zai ɗauki mutum 30,000.
Ya ce za a yi amfani da wurin wajen tsare "miyagun baƙin haure waɗanda barazana ce al'ummar Amurka."
An daɗe ana amafani da tsibirin Guantanamo wajen ajiye ƴan ci-rani, amma ya fi yin suna ne wajen tsare mutanen da ake zargi da hannu a harin da aka kai wa Amurka na ranar 11 ga watan Satumban 2001.
Wannan bidiyo ya yi bayani kan sansanin na sojin Ruwan Amurka wanda suka karɓa haya daga ƙasar Cuba tsawon fiye da shekara 100.



