'Yan biyun da likitoci 100 suka raba su ta kai ta hanyar fasaha

Bayanan bidiyo, 'Yan biyun da likitoci 100 suka raba su ta kai ta hanyar fasaha
'Yan biyun da likitoci 100 suka raba su ta kai ta hanyar fasaha

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An samu nasarar yi wa wasu ƴan biyun da suka haɗe ta kai tiyata a Brazil, ta hanyar amfani da fasahar da virtual reality.

An yi wa yaran ƴan shekara uku Bernardo da Arthur Lima tiyatar ne a birnin in Rio de Janeiro, bisa sa ido da bayar da umarnin daga likitoci a asibitin Great Ormond Street da ke Landan.

Tawagar likitocin ta shafe watanni suna fahimtar yadda za su yi amfani da fasahar virtual reality din don raba ƴan biyun.