...Daga Bakin Mai Ita tare da matar Farfesa Noor ta Jamilun Jidda

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
...Daga Bakin Mai Ita tare da matar Farfesa Noor ta Jamilun Jidda

A shirinmu na ...Daga Bakin Mai Ita na wannan mako hira da Zainab Barka, wadda ta fito a matsayin Matar Farfesa Noor a cikin shirin Jamilun Jidda mai dogon zango.

An haifeta a garin Fatakwal na jihar Rivers, ta yi karatu mai zurfi, inda ta yi digirinta na farko a fannin injiniyanci jami'ar Maiduguri, sannna ta yi digirinta na biyu a fannin fannin albarkatun ruwa a Jami'ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Minna.

Ta ce tun tana ƙarama take sha'awar duk wani abu da ya shafi nishaɗantarwa, amma saboda ta san a gida ba za a bari ta yi film ba saboda ƙarancin shekarunta ya sa ta haƙura.

Amma bayan ta yi aure ta haifi ƴaƴa sai ta yanke hukuncin komawa domin cimma burinta na yin film.

Ta ƙara da cewa kafin ta fara film sai da ta je makaranta ta yi wasu kwasa-kwasai a kan film, domin ta samu madafa a harkar.

Ta ce ta fara film ne a kudancin Najeriya kafin daga baya ta koma fitowa a finafinan arewacin ƙasar wato Kannywood.