...Daga Bakin Mai Ita tare da Janaral BMB
...Daga Bakin Mai Ita tare da Janaral BMB
A cikin shirin Daga Bakin Mai Ita na wannan mako mun kawo muku tattaunawa da fitaccen tauraron fim ɗin Hausa Bello Mohammed Bello, wanda ak fi sani da Janaral BMB.
BMB, wanda ya daɗe yana harkar fim, ya ce akwai wasu damarmaki da ya yi wasa da su a baya, waɗanda yanzu suke sa shi cizon yatsa.
Ɗan asalin garin Jos, ya shaida wa BBC abin da ya sanya ya yi watsi da ƙudurinsa na zama babban soja don ƙashin kansa.



