Bayern ta shiga jerin masu neman Vuskovic, AC Milan na zawarcin Scott

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Bayern Munich na zawarcin ɗan wasan bayan Brighton, Luka Vuskovic mai shekara 19, yayin da Chelsea da Barcelona suma ke sa ido kan ɗan wasan na Croatia. (Teamtalk)

Bayern Munich ta sake tattaunawa da ɗan wasan tsakiya na Manchester United, JJ Gabriel mai shekara 16, amma ba ta gabatar masa da tayi a kansa ba saboda ana ganin yana son komawa ƙasar Spain, inda ake ganin Barcelona da Real Madrid ne ke kan gaba wajen zawarcinsa. (Sky Sports Germany)

AC Milan na son ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Bournemouth, Alex Scott mai shekara 23, inda har yanzu ta da sha'awar ɗan wasan na Ingila duk da yadda ake ganin darajarsa na ƙaruwa. (Tuttomercatoweb)

FC Porto ta ɗara kuɗin da ta ke buƙata kan ɗan wasan gaba na Brazil, William Gomes mai shekara 20, zuwa Yuro miliyan 100 (fam miliyan 85) yayin da Liverpool ke nuna sha'awar ɗaukar sa. (A Bola)

Liverpool na kuma zawarcin Jules Kounde na Barcelona, ​​inda ƙungiyar ta La Liga ke shirin sauraron tayin fam miliyan 60 kan ɗan wasan bayan na Faransa. (Fichajes)

Chelsea na ci gaba da zawarcin ɗan wasan tsakiya na Monaco, Lamine Camara mai shekara 22, bayan da ta ƙasa samunsa a lokacin bazara; sai dai ƙungiyar ba za ta biya kuɗin da ƙungiyar ta Ligue 1 ta saka masa ba, wato Yuro miliyan 70 (fam miliyan 59), ga ɗan wasan na Senegal. (Goal)

Manchester City ta yi yunƙurin ɗaukar ɗan wasan gaba na Amurka mai shekara 17, Mathis Albert, daga Borussia Dortmund a lokacin bazara. (Goal)