Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muhimman abubuwan da ke hana mata tasiri a siyasar Najeriya
A Najeriya, ana ci gaba da tattaunawa kan yanayin yadda ake damawa da mata a siyasar Najeriya, inda wasu, musamman matan suke cewa ba sa samun damar riƙe madafun iko a ƙasar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shirye-shiryen babban zaɓen 2027, inda matan suke ƙara zafafa kiraye-kirayen lallai a ba su dama.
Gamayyar ƙungiyoyin mata masu kaɗa ƙuri'a a ƙarƙashin ƙungiyar Nigerian League of Women Voters (NILWV) ta miƙa takardar ƙorafi ga majalisar dokokin ƙasar, inda suka yi kira da a ware wa mata wau kujeru na musamman a Najeriya.
A wani taron ƙungiyoyin mata daga jihohi 36 da aka yi a babban birnin ƙasar Abuja a bara, mata sun buƙaci a ware wa mata kujera 37 a majalisar wakilai, da kujera 37 a majalisar dattawa, a matakin jihohi suna su a ware kujera 108, wato kujeru uku daga kowacce jiha.
Kakakin majalisar wakilan Najeriya Tajudeen Abbas, wanda ya halarci taron, ya jinjina wa ƙungiyoyin mata da matasa da masu buƙata ta musamman, inda ya ce yin hakan zai ƙara ƙarfafa samar da daidaito a ƙasar, da tabbatar da ana tafiya da kowa a harkokin mulki.
Hajiya Fatima Zakari ita ce mataimakiyar ƙungiyar League of Women Voters ta ce suna fafatukar ce domin ganin ana damawa da mata a siyasa da mulki, sannan ta yi fata za su samu nasara.
Shin hakan zai samu?
Ƙudirin dokar dai na buƙatar amincewar kashi biyu cikin uku na ƴan majalisun kasar, haka zalika ana buƙatar amincewa da dokar a kashi biyu cikin uku na majalisun jihohi wato jihohi aƙalla 24 cikin 36.
Bayan majalisun sun amince, wajibi ne majalisun dokoki suma su amince ƙarƙashin sashe na 9 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Wannan ya sa ake ganin aiki ne ja a samu damar tabbatar da ƙudurin da zai ware wa mata kujeru a majalisun tarayya da na jihohi.
A wani ɓangaren kuma, wasu na ganin zai yi wahala a ware wa mata kujeru na musamman, domin a cewar su, akwai wasu ƙungiyoyi da dama, irin nakasassu da suma za su buƙaci a ware musu kujeru.
'Muna ganin ƙalubale'
Shugabar mata ta jam'iyyar ADC ta ƙasa, Naomi Lassara Abel ta yi kira da a tabbatar ana damawa da mata da matsa a harkokin siyasa da mulki.
Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar game da wani taron ƙara wa juna sani kan muhimmancin damawa da matasa a harkokin siyasa a hedkwatar ADC da ke Abuja, inda ta ce cigaban Najeriya ta dogara ne a kan shirin matasa da mata na shiga harkokin shugabanci a ƙasar.
Sai dai ƴar siyasar ta bayyana cewa duk da kasancewar mata jigo ne a siyasar ƙasar, ba sa samun damar bayyana fasaha da ƙwarewarsu wajen gudanar da mulki a matakai daban-daban na ƙasar.
''Kamar yadda muka sani ana mana kallon kamar muna da rauni ne haka. Tun farkon siyasa musamman a Najeriya, mata da yawa ba sa shiga a dama da su ba. Sai a shekarun baya-bayan nan ne suka fara shiga harkar siyasa,'' in ji Naomi.
Naomi Lassara ta bayyana wasu abubuwa da ta ce suna cikin ƙalubalen da mata ke fuskanta kamar haka:
- Al'adu
- Addini
- Ƙudi
- Raunin mata
- Yawan maza a harkar
Naomi wadda ta taɓa yin takarar majalisar jihar Gombe domin wakiltar mazaɓar Kaltungo ta Kudu da ma majalisar tarayya, ta ce ta yi takara, sannan ta yi shugabancin jam'iyya, don haka ta ga komai.
"Idan kin fito takara sai ki ga maza da yawa sun fito, don haka kafin ki fito ki nuna ƙwanjinki, sai ki ga sun kwashe komai,'' in ji ta.
Ta ƙara da cewa mata sun fi yawan ƙuri'u a zaɓen Najeriya, "Muna ƙoƙarin zaɓen kanmu. Ni na yi takara kuma lallai mata sun ban goyon baya sosai. Amma in maka misali, za ka ga shugabannin jam'iyya a mazaɓa, wataƙila a kujeru 18, ka ga mace ɗaya ce kacal wato shugabar mata.''
Ta ƙara da cewa idan ya kasance a babban zaɓen mazan sun fi yawa, to duk yawan ƙuri'ar mata ta tafi wajen mazan.
Sai dai ta ce ana samun cigaba sosai a yanzu, domin a cewarta, ƙungiyoyin mata da jam'iyyu na ƙoƙari sosai wajen wayar da kan mata da janyo su cikin harkokin siyasa.