Harin Tudun Biri: 'Gawarwaki kawai muka gani kamar an kwanta barci'

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Harin Tudun Biri: 'Gawarwaki kawai muka gani kamar an kwanta barci'

Ranar 3 ga watan Disamban 2023 ya kamata ta zamo ta farin ciki ga al'ummar Tudun Biri lokacin da suke bikin zagayowar Maulidi.

Sai dai wasu bama-bamai guda biyu da sojojin Najeriya suka jefa kan ƙauyen ya sauya batun.

Sama da mutum 83 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu rauni.

Har yanzu mutanen ƙauyen na ƙoƙarin yadda za susake gina rayuwarsu bayan abin da ya faru.