Mutanen da suka yi gadon haƙar kabari da wankan gawa
Mutanen da suka yi gadon haƙar kabari da wankan gawa
Sama da shekara 50, wasu iyalai suka sadaukar da rayuwarsu wajen kula da wata babbar maƙabarta a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Sun kwashe waɗannan shekaru suna yin wannan aiki na haƙa kabari da wankan gawa, ba tare da ana biyansu ba, sai dai tallafin da ba za a rasa ba daga ƴan'uwan mamatan.
Akwai buƙatar su kasance kodayaushe a wajen aikin saboda musulmai ba sa jinkirta rufe mamaci.
A 1970 ne Ibrahim da Adamu iyalan gidan Abdullahi suka soma aikin na kula da maƙabarta.



