Ku San Malamanku tare da Sheikh Shaya'u Yusha'u Ahmad

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Sheikh Shaya'u Yusha'u
Ku San Malamanku tare da Sheikh Shaya'u Yusha'u Ahmad

An haifi Sheikh Shaya'u Yusha'u Ahmad a ƙaramar hukumar Gashuwa ta jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya, wanda ke zaune a garin Bauchi.

Ya fara karatun Ƙur'ani a gaban mahaifinsa a Gashuwa, inda daga baya ya koma wajen ɗan'uwan mahaifin nasa a Potiskum.

Ya yi karatu a kwalejin nazarin addinin Musulunci da ke garin Bauchi a shekarar 1999. Ya samu shiga jami'ar Musulunci ta Madina a shekarar 2000.

Shehin malamin ya samu ƙwarewa a fannin alƙalanci da kuma siyasar Musulunci a Madina.